Labaran siyasa

Na fice daga APC saboda gwamnoni sun fi karfin Buhari – Shehu Sani

– Sanata Shehu Sani, ya alakanta ficewarsa daga APC da gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari na juya gwamnonin jam’iyyar

– Shehu Sani ya tabbatar da cewa zai yi takara a zabe mai zuwa, kasancewar akwai jam’iyyun da suka dade da tsayar da shi amma a lokacin bai karbi tayinsu ba

– Ya ce tuntuni yayi niyyar ficewa daga jam’iyyar, amma uwar jam’iyyar ta kasa ta dakatar dashi tare da yin alkawarin dai-daita rikicinsa da jam’iyyar jihar

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattijai ta kasa, Sanata Shehu Sani, fayyace dalilin ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki, yana mai alakanta ficewar tasa da gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari na juya gwamnonin jam’iyyar.

Kamar dai yadda Sanaran ya shaidawa BBC, ya ce tuntuni jam’iyyar APC ta kauce daga ainihin manufofi, kudurori da kuma akidojinta, wanda ma har hakan yasa talakawa ke sonta komai wuya, amma sakacin gwamnonin jihohin da take mulki na yi ma jam’iyyar rikon sakainar kashi, ya sa hatta shi kansa ma shugaban kasar bashi da katabus.

Sai dai duk da cewa Sanata Shehu Sani bai samu tikitin komawarsa takarar kujerar sanatan a karkashin jam’iyyar APC ba, ya tabbatarwa BBC cewa zai yi takara a zabe mai zuwa, kasamcewar akwai jam’iyyun da suka dade da tsayar da shi amma a lokacin bai karbi tayinsu ba.

Shehu Sani ya alakanta ficewar tasa da yadda aka gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar a jihohi ta yadda sai abin da gwamnoni suka zaba ba jama’a ba shi ne uwar jam’iyyar ma a tarayya za ta amince da shi.

Sanatan ya ce: “Tun a baya na yi yunkurin ficewa daga APC, a lokacin da guguwar canjin shekarar yayi awon gaba da wasu takwarorina a majalisa, amma shuwagabannin jamiyyar na kasa suka dakatar da ni, ta hanyar yi min alkawarin sasanci a cikin lamarin, sai dai ina ga kamar yaudara ce kawai a cikin alkawarin nasu.”

Da yawa na ganin cewa dan majalisar dattawan, ya yanke wannan hukuncin nasa ne sakamakon rikicin da ke ruruwa tsakaninsa sa gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, da kuma jam’iyyar APC a jihar. Sai gashi yanzu jam’iyyar ta mika sunan Mallam Uba Sani a matsayin dan takararta na sanatan Kaduna ta tsakiya mai makon Shehu Sani Kafin hakan hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja tun a baya ta sanar da cewa Shehu Sani shi kadai ne aka wanke da zai yi takarar kujerar, matakin da gwamnatin jihar da reshen jam’iyyar na jihar suka ki amincewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button