Labaran Duniya

Na Fi Samun Kudi A Safarar Wiwi, inji Wani Dilan Wiwi

Rundunar ‘yan sanda na musamman da ke Minna jihar Neja ta samu nasarar cafke wani mutum mai suna Abdullahi Usman dan shekara 20 a Anguwar Roka cikin karamar hukumar Maitumbi Bosso ta jihar, bisa mallakar makamai masu hatsari da kuma miyagun kwayoyi. An bayyana cewa shi dai wanda ake zargi, shi ne shugaban ‘yan daban Anuwar Roka da ke cikin karamar hukumar Maitumbi Bosso ta jihar. Wanda ake zargin ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi cewa, ungiyarsa tana da layan da take amfani da ita wajen kaucewa duk wanda zai tsayar da su a kan hanya.“Muna da laya wacce muke amfani da ita wajen yakar duk wani wanda ya yi kokarin tsaida mu a kan yanya, layarmu ba ta taba yi mana rashin aiki ba sai da na tsinci kaina a tarkon ‘yan sanda,” inji shi.
Usman ya tabbatar da cewa, yana saida wiwi sannan kuma yana samun kudi a cikin wannan haramtacciyar kasuwanci fiye da aikin gidan biredi,”inji wanda ake zargi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda Muhammad Abubakar ya bayyana cewa, Usman shi ne shugaban ‘yan daban Anguwar Roka. A ciwarsa, an samu gunshin wiwi guda 81, takobi guda daya, gurori guda hudu, wuka mai kaifi guda biyu, adda guda daya da kuma layoyi daga hannun wanda ake zargi. Ya kara da cewa, za a kai shi kotu idan aka kammala bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button