Labaran Duniya

Mutum 10 da suka kere kowa kudi a Najeriya

Kamar dai yadda aka sani a kasar Najeriya, nahiyyar Afirka da ma duniya baki daya, Alhaji Aliko Dangote yana daya daga cikin mutanen da za su daga dan yatsa idan anzo maganar kudi.
Kudi wanda hausawa ke cewa masu gidan rana, su na tsonewa mutane idanu, sanadiyar hakan ne ya sanya aka bincike domin gano wadanda suka yi fice wajen tarin dukiya a sassa daban na duniya.
Mutum 10 da suka kere kowa kudi a Najeriya

Dangote ya fi kowa kudi a Najeriya


Shafin NAIJ.com ya bankado daga kididdiga ta binciken jama’a akan wadanda suka kere kowa kudi a nan Najeriya, wanda kuma ko shakka ba bu Alhaji Aliko Dangote ya kere kowa.A wata ruwaya daga maganganun al’umma sun bayyana cewa, ana yiwa Dangote mai kudin bakar fata a duk duniya domin a cewar su indai mutum baki ne to kuwa Dangote ya fi shi kudi.
Ga jerin sunayen mutane 10 na Najeriya da suka yi fice wajen tarin dukin da masana’antunsu ko kuma sana’ar su:
1. Alhaji Aliko Dangote – Mai gidauniyar Dangote
2. Mike Adenuga – Mai kamfanin Con oil da kamfanin sadarwa na Globacom
3. Femi Otedola – Mai kamfanin Forte oil
4. Orji Uzor Kalu – Mai gidauniyar Slok
5. Cosmos Maduka – Mai gidauniyar Coscharis
6. Jimoh Ibrahim – Mai kamfanin inshora na Nicon da kuma Global Fleet
7. Jim Ovia – Bankin Zenith da kamfanin sadarwa na Visafone
8. Pascal Dozie – Kamfanin sadarwa na MTN da bankin Diamond
9. Oba Otudeko – Gidauniyar Honeywell, kamfanin mai na Pivotal da kamfanin sadarwa na Airtel
10. Alhaji Sayyu Dantata – Gidauniyar mai na MRS


Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button