Labarai

Muna Kira ga Al’ummar Nijeria Kafin 6 ga watan Nuwamba Kowa ya tanadi kayan abincinsa – NLC ta shawarci ‘yan Nigeria

 Ministan kwadago da shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC
Ministan kwadago da shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC 

Shuwagabannin kungiyoyin kwadago, sun shawarci ‘yan Nigeria da kowa ya tanadi kayan abinci, gabanin fara yajin aiki da kungiyoyin za su shiga a ranar 6 ga watan Nuwamba
Kungiyar kwadagon, ta yi nuni da cewa, tabbatar da N30,000 a matsayin sabon tsarin biyan mafi karancin albashi, shi ne kadai zai dakatar da su daga shiga yajin aikin – Ayuba Wabba, ya ce kungiyoyin na sane da wani tuggu da ake shiryawa don ganin bayan shuwagabannin kungiyoyin A jiya Juma’a, shuwagabannin kungiyoyin kwadago, a wani zama da suka gudanar a jihar Legas, sun shawarci ‘yan Nigeria da kowa ya tanadi kayan abinci, gabanin fara babban yajin aiki na fadin kasar da kungiyoyin za su shiga a ranar 6 ga watan Nuwamba. Kungiyar kwadago dai ta ja layi ga gwamnatin tarayya, inda ta ce lallai sai dai N30,000 ya zama mafi karancin albashi ga ma’acin kasar. Sun yi gargadi cewa za su fara wannan yajin aikin ba sani ba sabo daga ranar Talata, har sai idan gwamnatin tarayya ta amince da wannan bukata ta su. Kungiyar kwadagon, ta yi nuni da cewa, tabbatar da N30,000 a matsayin sabon tsarin biyan mafi karancin albashi, shi ne kadai zai dakatar da su daga shiga yajin aikin.

Wannan tabbaci daga kungiyoyin kwadago ya zo ne biyo bayan wata takardar umurni da gwamnati ta karbo daga hannun kotun masana’antu, da ke haramtawa kungiyoyin shiganyajin aikin, sai dai kungiyoyin sun ce sam ba su ma san da wannan umurni na kotun ba.

A wani zaman tattaunawa da manema labarai, jim kadan bayan zaman kwamitin gudanarwa na kungiyoyin kwadagon da suka hada da NLC, TUC da kuma ULC, tuni suka cika duk wasu sharudda na shiga yajin aikin, sun masu cewa gwamnati na da damar dakatar da shirin daga nan har 11pm na ranar Litinin. Da ya ke karanta takardar bayan kammala taro ga manema labarai, a madadin sauran shuwagabannin kungiyoyin kwadagon, shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba, ya ce kungiyoyin na sane da wani tuggu da ake shiryawa don ganin bayan shuwagabannin kungiyoyin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button