Labaran Duniya

Motoci 10 da su ka fi jirgin sama tsada, hotuna

Jama’a da dama za su yi matukar mamakin jin cewar akwai motocin hawa da su ka fi jirgin sama tsada, musamman ganin cewar jirgi ya fi girma da kawa a tsarin kira idan aka kwatanta shi da mota.

Hausafinest.com.ng ta ci karo da jerin wasu motoci 10 da suka fi jirgin sama tsada. 10.

Bugatti Chiron – Dalar Amurka miliyan $2.7m (miliyan N826m)

Kamfanin Bugatti ne ya kera wannan mota da ake ikirarin babu mota kamar ta a bangaren gudu da kawatawa.

Farashin motar na farawa daga dalar Amurka miliyan $2.7m zuwa dalar Amurka miliyan $3m.

Bugatti Chiron

 9. Pagani Huayra BC – Dalar Amurka miliyan $2.8m (Naira miliyan N856m) Ita ce mota ma fi tsada da kamfanin Pagani ya taba kerawa.

An fara ganin motar ne a shekarar 2016 a bikin bajakolin motoci a Geneva, kasar Switzerland.

Pagani Huayra BC Source:

8. Ferrari Pininfarina – Dalar Amurka miliyan $3 (Naira miliyan N918m)

An kirkiri wannan mota ne a shekarar 2013 domin tunawa da mutumin da ya fara kirkirar motocin Pininfarina.

Mutane 6 ne kacal su ka mallaki motar a duniya, kuma su ma kamfanin ne ya zabe su. Hakan ya saka ta daya daga cikin motoci ma fi karanci a duniya.

Ferrari Pininfarina
7. Aston Martin Valkyrie – Dalar Amurka miliyan $3.2 (Naira miliyan 979)

Har yanzu kamfanin wannan mota bai fitar da farashinta ba saboda sai shekarar 2019 za ta shiga kasuwa.

Sai dai masana motoci da farashinsu sun yi kiyasin cewar kudinta ba zai taba gaza Dalar Amurka miliyan $3.2 ba.

Aston Martin Valkyrie

 6. Bugatti Veyron – Dalar Amurka miliyan $3.4 (Naira biliyan N1.04bn)

 Mota ce kirar kasar Jamus da aka canjawa fasali da fasaha har sau hudu tun bayan shigowar ta kasuwa a shekarar 2005. Ta na cikin motoci masu masifar gudu a duniya.

Bugatti Veyron 5. Lykan Hypersport – Dalar Amurka miliyan $3.4 (Naira biliyan N1.04)

Daya daga cikin dalilin tsadar wannan mota shine na cewar an yi fuskar fitilar ta ne da gwal. Kamfanin W motors da ke kasar Lebanon, a yankin Larabawa, ya fara kera motar.

Lykan Hypersport

 4. McLaren P1 LM – Dalar Amurka miliyan $3.6m (Naira biliyan N1.1)

Ita dama an kera ta ne domin wasu tsirarun masu saya daga kasashen Amurka, Japan, Ingila da Daular larabawa. Injina biyu gare ta, kowanne na da fulogi 8.

 An kewaye injinanta da zinare.

McLaren P1 LM  3. Lamborghini Veneno Roadster – Dalar Amurka miliyan $4.5m (Naira biliyan N1.38bn)

 Kalmar Veneno na nufin guba ko dafi a Hausa.

Kamfanin lamborghini ya kirkiri wannan mota ne domin murnar cika shekaru 50. Motar na tafiyar mayil 60 a sa’a daya cikin dakika 2.9 kacal.

Lamborghini Veneno Roadster
 2. Koenigsegg CCXR Trevita – Dalar Amurka miliyan $4.8m (Naira biliyan N1.47bn)

 Ita ce mota ma fi tsada da ta fara samun damar taka kan titi da izinin kamfanin kera motoci na duniya. Jikinta na zallar gwal ne.

Koenigsegg CCXR Trevita

1. Sweptail Rolls Royce – Dalar Amurka miliyan $13m (Naira biliyan N3.99bn)

Kafin ka kasa rufe baki saboda mamakin tsadar wannan mota, ya kamata ku sani cewar kamfanin wannan mota ya kera ne bisa tsarin da wani mutum ke so.

Sai dai har yanzu kamfanin ya ki sakin bayanai a kan wannan mutum.

Sweptail Roll Royce
Karin wani abin mamaki a kan wannan mota shine gurin zaman mutum biyu kacal ta ke da shi kuma duk kofofin jikin motar na’urori masu kwakwalwa ne a manne a jiki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button