Labaran wasanni

Monaco ta nada Henry Thierry sabon manaja

Kungoyar Kwallon kafar Monaco da ke France ta nada tsohon tauraron kungiyar Arsenal da Barcelona, Thierry Henry a matsayin mai horar da ‘Yan wasa domin maye gurbin Leonardo Jardem da ta kora saboda kungiyar ta kasa kokari a karkashin sa a cikin wannan kakar wasanni.
Da ya lashe kofin Turai da na duniya da kasar Faransa, yana aiki ne a matsayin mataimakin mai horar da kungiyar kasar Belguim a karkashin Roberto Martinez tun shekarar 2016, wanda ya taimaka musu zuwa matsayi na uku a gasar cin kofin duniyar bana.
 Henry mai shekaru 41 ya sanya hannu kan kwangilar da zata kai shi watan Yunin shekarar 2021 a kungiyar da ya fara wasan sa a matsayin kwararen dan kwallo.
 Henry na daga cikin yan wasan da suka samu horo tun suna kanana a kungiyar Monaco, yayin da ya fara buga mata wasa a shekarar 1994, inda a shekarar 1997 zuwa 1998 ya jefa kwallaye 7 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, a karkashin jagorancin Arsene Wenger, nasarar da ta kaisu wasan kusa da na karshe da suka sha kaye a hannun Juventus.
Bayan ya kwashe shekaru 5 a Monaco, Henry ya koma kungiyar Juventus da Arsenal da Barcelona kafin karkarewa da New York Red Bulls.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button