Labaran wasanni

Mohammad Salah Zai Iya Barin Liverpool Idan Ba Su Ci Kofi Ba, Cewar Kocin EgyptKoch din  tawagar ’yan wasan kasar Masar, Jabier Aguirre, ya bayyana cewa dan wasan kasar ta Masar, Muhammad Salah, zai iya barain Liverpool idan dai har kungiyar bata kawo karshen rashin cin kofin da takeyi ba. 
Mohammad Salah dai yaji dadin kakar wasansa ta farko a kungiyar kwallon kafa ta Liberpool inda ya karya tarihi kala-kala kuma ya zura kwallaye 44 a kakar ciki har da kwallaye 32 dayaci a gasar firimiyar Ingila. 

Sai dai duk da kokarin da Salah yayi a kungiyar amma bata samu damar lashe kowacce irin gasa ba kuma ta kammala gasar firimiya a matsayi na hudu yayinda rabon kungiyar da lashe kowacce irin gasa tun shekara ta 2012. 

Sai dai kociyan tawagar ta ‘yan wasan Masar din ya bayyana cewa idan har kungiyar bata samu nasarar lashe kofi ba anan kusa tabbas Salah zai nemi wata kungiyar ya shiga saboda babban dan wasane shi kuma yana bukatar cin kofi.

Salah zai iya barin kungiyar nan da shekara biyu idan har basu samu nasarar lashe kowanne irin kofi ba kuma kociyan kungiyar yasan da haka shine yasa suka dage domin ganin sun samu nasara a wannan shekarar” in ji kociyan kasar ta Masar. 

Ya kara da cewa Liverpool babbar kungiya ce wadda take da tarihin lashe kofuna tun asali amma kuma a ‘yan shekarun baya abubuwa sun canja kuma akwai bukatar a samu canji idan anaso manyan ‘yan wasa irinsu Salah suci gaba da zama A kwanakin baya dai Muhammad Salah ya kara sabon kwantaragi a kungiyar ta Liberpool wanda zaisa ya zauna har shekara ta 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button