Labaran wasanni

Mikel Obi bai yi ritaya daga buga wa Najeriya wasa ba

Dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya, John Mikel Obi bai yi ritaya daga buga wa kasar wasan kasa da kasa ba kamar yadda mai magana da yawun tawagar ya sanar.

Wannan na zuwa ne bayan Najeriyar ta buga wasanni har guda uku a jere ba tare da Kaften Obi ba da ke taka leda a Kungiyar Kwallon Kafa ta Tianjin ta China.
Tun bayan dawowar Najeriya daga Gasar Cin Kofin Duniya a cikin watan Juni, raban da Obi ya buga wa Najeriya wani wasa.
An bai wa dan wasan damar murmurewa daga jerin raunin da ya samu kuma a yanzu ya koma fagen daga,  amma duk da haka ba ya cikin tawagar ‘yan wasa 23 da za ta kece raini da Afrika ta Kudu nan gaba. 
Sai dai mai magana da yawun Super Eagles din, Toyin Ibitoye, ya ce, dan wasan bai yi ritaya ba kuma har yanzu yana nan a matsayinsa na kaften din Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button