Adon Gari

Mene Ne Dalilinki Na Hana Mijinki Kara Aure?Allah ya sanya namiji shi ne da hakkin tsayuwa kan iyalansa, kuma tun a farko shi ke da nauyin bada sadaki, muhalli, ciyarwa, tufatarwa, kula da lafiyar su da baiwa iyalansa kariya da tsaro yadda za su zauna cikin aminci da natsuwa, wato dai miji ake fatan ya yi ta kai kawo wajen daukan dawainiyar iyalansa. 
A karantarwar Addinin Islama ta fito fili wajen tabbatar wa maza auren macce guda da kuma damar karawa zuwa mata biyu ko uku ko hudu in ya san zai iya yi masu adalci kuma zai iya kula da su, amma idan ya san ba zai iya yin adalci ba to ya auri mace daya.
 Allah ya hore mu a kan cewa ka da kowa ya karkata zuwa ga nuna fifiko a fili na son wata cikin matansa har ya bar dayar ko sauran matan su zama marasa amfani a cikin gidansa, wanda kowa ya tara mata amma ya ki yi masu adalci to a ranar alkiyama zai  tashi sashin jikinsa a shanye. Dan haka sai mu kula da sauke nauyi matayenmu.

Mu sani fa muna cikin wani zamanin da ba mai yi maka musu in ka ce mata na da matukar yawa fiye da maza, amma bisa hikimar Allah duk wannan yawan matan an yi masu tanadin wurin shiga shi ne an yarda ko wani namiji daya ya auri har mata guda hudu idan yana da hali kuma yana iya yin adalci. 
Madallah da wannan dama don za ta taimaka wa ‘yan uwa mata kowa ta samu mijin aure da yardan Ubangiji. Yanzu dan uwa yadda kididdigar masana ke nuna yawaitar mata, me kake tunani a nan gaba zai faru in kowani namiji  ya ki aure ko ya kara aure? Kuma iyaye na mata in kuka kasa, kuka tsare, kuka toshe kofar karo aure ina makomar ‘ya’yanku ‘yan mata da kannen ku ko ‘ya’yun ku zaurawa da mutuwar aure ko mutuwar miji ya jawo mata zawarci?
Annabi (S.A.W) yana cewa: 
Duk wanda kuka amince da addinisa da halinsa idan ya zo neman aure, to ku aurar masa. A nan ba a yi mana nuni da sai mai kudi, ko mai mulki ko wani dan boko ba, a’a mai addini da hali mai kyau ake so. In aka ki bin wannan umarni to fitina da barna mai yawa za su wanzu a bayan kasa. Ya kamata mu natsu sosai mu ga yadda rashin damar yin aure ke jefa matansan mu maza da mata cikin shaidanci da sabon Allah. Kuma haka iyaye ke zaune cikin zulumi da takaicin ganin ‘ya’yansu manyan ‘yan mata ba aure. 
Ga samari na ta cizon yatsa, kamar ka ce a yi masu rukiyya in suna hirar barkwanci a kan aure, har ka ga ‘yan mata tika-tika sai shafe-shafe da shiga dandalin sada zumunta na zamani ba ranar aure, har jinkiri ya sa ta fara neman maganin jinnu da shiga bokaye. 
Ga zaurawa nan ta ko ina, idan aka ce a yi kirgen zaurawa ne to kusan ko wanni gida akwai, ga kuma fitsararrun mata ‘yan ina da biki, abun dai sai addu’a ba dadin ji a cikin wannan zamani.

Sai dai wani abin mamaki shi ne har zuwa yau al’ummarmu da shugabanninmu duk an kasa daukar matakin wannan matsala wanda tun kana jin labarin yawan mata marasa aure a can wata kasa, yanzu har ka fara hangota a hankali yau gashi ta iso garin ku ko kaima har a ce ga kanwarka, ko ‘ya’yanka ko diyarka ko wata marainiya a unguwarku a zaune ba aure ba kuma manemin auren. 

Da zamu nemi sanin alkaluman yawan mata da mazan da a musulunce ya kamata a ce suna dakin miji a kasar nan sai ka rasa ta ina za ka fara. Wato ina nufin sai an yi muhawara kafin a samu matsaya, a ce da ‘yan sakandare za a fara? Ko ‘yan jami’a? Ko ma wanda sam ba su taba yin boko ba?

Jama’armu ana cewa cikin maza da mata akwai masu ilimi ko kaji ana aibata mata ‘yan yawon talle ana cewa suke yin bandaro, wato sun girma ba aure ba manemi, yanzu ga maza da mata ‘yan boko wasu ma sun hada biyu ga ilimin addini ga na boko ana ganin su sun makale babu aure, ko har zuwa yaushe za su yi oho! A haka har a tsufa ba a yi aure ba.

Mu sani aure fa ibada ne kuma hanyar samun karin natsuwa ne da aure ake tara zuriya, ake more rayuwa ta hanyar debe kewa, ake samun cikar daraja ta mutumtaka da kwarjini da daukaka da kuma lada mai yawa. Har da matasa an masu umarni da su yi aure, yin aure da wuri yana da kyau, kuma iyaye an dora maku hakkin aurar da ‘ya’yanku maza da mata. Ya halatta in ta gagara to kai da kanka ka nema wa diyarka miji, sa’annan magidanta kuma an ce ku kara iyali wato ya zama matanka biyu ko uku ko hudu idan za ku iya yin adalci. To me muke jira ba za mu kara ba?

Tabbas duk matar da ke hana mijinta kara aure to ta sani ta cuci kanta. Domin ki sani cewa kwanda ki bari ya kara aure da ya fada neman matan banza. Allah ne ya halattawa maza auren mace fiye da daya har zuwa hudu idan za su iya yin adalci. Ke kuma da kika hana majinki kara aure, kina ja da maganan Allah kenan kuma dole za ku rabu da shi ko dai mutuwa ta raba ko kuma zama ya raba, amma basa ku tabbata tare ba. Mutane mu yi hattara, mu sani cewa yawaitar mata marasa aure zai iya jawo mana matsaloli a cikin al’ummarmu. Don haka maza a daure a kara aure. Su kuma matan su daure a rage kishi da buri, a duk yadda kika kai da son duniya, to dole wata rana za ki barta, Allah ya sa mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button