Labaran siyasa

Me ya hana Ganduje zuwa majalisar Kano da kansa?

Gwammnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kauracewa kwamitin binciken da majalisar jihar Kano ta kafa kan bidiyon zargin karbar rashawa daga ‘yan kwangila, inda ya tura kwamishina watsa labarai na jihar Malam Muhammadu Garba ya wakilce shi.
Majalisar ta gayyaci gwamna ganduje domin ji daga bakinsa kan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, inda a ciki aka nuna ‘gwamnan’ yana karbar bandir-bandir na dalar Amurka daga wajen ‘yan kwangila.
Tun da safiyar Juma’ar nan ne, ‘yan jarida da kungiyoyin al’umma da kuma ‘yan kallo suka hallara a harabar majalisar, ana dakon zuwan gwamnan
Wannan layi ne
To sai dai kwamishin watsa labarai Malam Muhammad Garba wanda ya wakilci gwamnan yace, gwamnan yana da zabi ya je da kansa ko kuma ya tura wakilci.
Ya kara da cewa Ganduje ya tura wakilci ne saboda girmama majalisar.
A jawabansa dangane da bidiyon, Malam Muhammad Garba ya musanta cewa bidiyon suna da inganci, ya ce an shirya su ne kawai domin a batawa gwamnan Kano suna, da kuma makarkashiyar siyasa, musamman yanzu da ake tunkarar zabukan 2019.
A makon da ya gabata dai dan jaridar da ya wallafa bidiyon ya bayyana a gaban kwamitin inda ya jadda cewa, bidiyon sahihai ne, sai dai bai bayyana daga inda ya same su ba.
Kwamitin na majalisar dokokin Kano da ke bincike kan zarge-zargen bai yi wa kwamishin tambayoyi ba, saboda a cewarsa ba kwamishina ake zargi ba, Gwamna Ganduje ake zargi, don haka shi ne kadai zai iya amsa tambaoyin da suke da su.
Kwamitin wanda ke karkashin Baffa Babba Danagudi ya ce zai je ya yi nazarin bidiyon, sannan zai cimma matsaya kan batun zuwa ranar Talata mai zuwa.
Karin haske
Tun da fari kwamitin majalisar dokokin jahar Kanon ya tura wa Gwamna Ganduje goron gayyata ne domin ba shi damar fadin abin da ya sani dangane da zargin da ake masa na karbar wasu damman daloli a cikin hotunan bidiyon, wadanda ake zargin cewa rashawa ne daga hannun wasu kamfanonin da ke yi wa gwamnatin jihar ayyukan kwangila.
Kwamitin ya bukaci gwamnan da ya tsara dukkan bayanansa a rubuce, wadanda zai gabatar masa, bayan wasu ‘yan tambayoyin da watakila ‘yan kwamitin za su masa, baya ga damar da kwamitin ya bai wa gwamnan ta zuwa da lauyoyinsa wajen jin bahasin.

Jan hankalin al’umma

Wannan batun zargin karbar rashawa da ake yi wa gwamnan jihar Kano dai shi ne babban abin da ke jan hankalin al’umma, kasancewar bangarorin al’uma da dama, musamman kungiyoyin farar-hula, sun zuba ido su ga yadda maganar za ta kaya.
Kwaamared Rabi’u Shamma shi ne shugaban hadaddiyar kungiyar matasa da ke rajin ci gaban jihar Kano, wadda ke bin diddigin binciken, wadda kuma ke da ra’ayin cewa muddin ana so a yi adalci, to kamata ya yi gwamna Ganduje ya sauka daga kan kujerarsa, ya koma gefe guda na wani lokaci.
A makon jiya ne kwamitin ya saurari bahasi daga Ja’afar Ja’afar, wato dan jaridar da ya wallafa hotunan bidiyon da nufin bankada, inda wasu yara ‘yan makarantar furamare suka yi zanga-zangar goyon baya ga gwamna Ganduje a gefen zauren majalisar dokokin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button