Labaran wasanni

Me Buhari Zai Yi Wa Harkokin Wasanni?

Jama’a ma’abota wasanni sun mika kiraye-kirayensu ga shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari.

Wadannan kiraye-kirayen nasu ya jibanci yadda za’a inganta fannin wasanni a Najeriya.

Muhammadu Bello wani mai sha’awar wasan kwallon kafa ne.

“(Muna so Buhari) ya gyara mana klub din Najeriya, a saka shuwagabanni masu adalci. Wadanda suka san kan kwallo, kuma a kira ‘yan wasa, muna da ‘yan wasa duka Afirka, babu ‘yan wasan da suka kai ‘yan Najeriya”.

Shi kuwa Liman Kasuwar Shanu a Ibadan cewa yayi “Ya kamata Buhari yayi gyara tsakanin ministan wasanni da shugaban hukumar wasanni na Najeriya. Bai yiwuwa a ce da minista, da shugaban hukumar wasanni ana rigima.”

Kungiyoyi da jama’a masu zaman kansu sunyi ta bayyana bukatunsu ga sabuwar gwamnati dake jiran gado a Najeriya, musamman ma bayan gani Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugabancin kasa. To tambayar anan itace shin shugaban zai iya sharewa kowa kukansa? Ko ma zai iya gudanar da aiki baki daya? Masu magana suka ce rana bata karya, sai dai uwar diya ta ji kunya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button