Martanin mutane bayan an ji labarin Atiku ya ci zaben PDP
Dazu ne dai labari ya isa Duniya cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP inda zai yi takarar Shugaban kasa da Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Ina taya Atiku murnar wannan nasara na samun tikitin PDP domin takarar badi. Na jinjinawa irin wannan namijin kokari da jajircewa na Atiku a fagen siyasa inda ya fara kafa sunan sa tun shekaru 25 da su ka wuce a lokacin Marigayi MKO Abiola.
– Inji Dele Momodu
Atiku ya nuna Gwamna Wike cewa akwai banbancin wanda ya koyi siyasa wajen Shehu Yaradua da kuma masu yi wa Abokan adawar su barazana a gaban Talabijin Duniya.
– Japheth Omojuwa
Wani Masoyin Rabiu Musa Kwankwaso kuwa cewa yayi:
Wata guda da su ka wuce na ji Dr. Hakeem Baba-Ahmed yana cewa manyan ‘Yan takaran Shugaban kasa da su ka fi karfi a PDP mutum 3 ne; Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Atiku Abubakar. Yanzu kam na fahimci gaskiya.
– Abubakar Dadiyata