Labarai

Manyan Malaman Izala sun kai ziyarar goyon baya ga gwamna Ganduje

Shuwagabannin kungiyar Izala reshen jahar Kano sun kai ziyara ga gwamnan jahar Kano a fadar gwamnati jahar, inda suka jadda masa goyon bayansu ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, musamman a yayin da yake tunkarar zaben shekarar 2019.
Wakilin mu na gidan gwamnata ya bayyana mana cewa shugaban Malaman Izala, Abdullahi Saleh Pakistan ne ya jagoranci tawagar Malaman zuwa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Alhamis 8 ga watan Nuwamba.

A yayin wannan ziyarar da suka kai masa, Malaman sun jaddada goyon bayansu a gareshi, sa’annan suka jinjina ma gwamnan bisa muhimman ayyukan da yake yi a jahar Kano, da ma ayyukan da yake yi ga addinin Musulunci.

Idan za’a tuna gwamnan jahar Kano ne babban hadimin addinin Musulunci a jahar Kano watau ‘Khadimul Islama’, wanda ko a satin daya gabata sai da gwamnan ya musuluntar da maguzawa da sama da dari biyu.

Sai dai jama’a da dama sun nuna rashin jin dadinsu da wannan ziyara, musamman a wannan lokacin da ake zargin gwamnan da karbar cin hanci da rashawa da suka kai dala miliyan biyar daga hannun wasu yan kwangiloli.
Masu irin wannan ra’ayi na ganin Malaman sun nuna goyon bayanzu ga gwamnan a fili, wanda a cewarsu kamata ya yi Malamai su kasance masu daidaita sahun al’umma ba wai su dinga goyon bayan masu mulki akan rashin gaskiya ba.

A wani labarin kuma, dan kwangilar daya baiwa Ganduje makudan kudaden nan har ma ya daukeshi wannan bidiyon ya bayyana ma majalisar dokokin jahar Kano cewa zai gurfana gabansu amma fa sai Gwamna Ganduje da shugaban Hisbah Aminu Daurawa sun halarci zaman.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button