Kannywood

Manyan jaruman kannywood sunyi tsokaci kan bidiyo na tsiraicin maryam Booth

Kamar yadda kuka sani a aranar Alhamis ne 7 ga watan Fabrairu masana’antar film ta Kannywood ta tashi da wani abun bakin ciki sakamakon wani ibtila’i da ya cika da daya daga cikin jarumanta mata wato Maryam Booth. 

An dai wayi gari ne aka tsinci wasu sun daura bidiyon tsiraicin jarumar zindir a shafin sadarwa ta Twitter, lamarin da bai yiwa mutane da dama dadi ba. 

A halin yanzu yawancin ‘yan fim da su ka ji labarin bullar bidiyon sun tausaya wa Maryam, su na fadin cewa ba laifin ta ba ne, kuma ba sabon abu ba ne yarinya ta fito daga wanka a bandaki tsirara a gaban kawar ta, musamman a cikin daki. 

Wasu daga cikin manyan jaruman  sun je shafukan zumunta ta Instagram inda suke lallashin Maryam tare da bata karfin gwiwar cinye wannan ibtila’i daya saukar mata, tare da yin Allah wadai da wadanda suka yada bidiyon. 

Falalu Dorayi a martaninsa ya ce: “Bana goyan bayan duk wata barna Yinta ko Yadata… Nafi yadda da umarnin Idan kaga Dan uwanka cikin Dabi’a mara kyau ka zamo mai masa Nasiha da jan hankali ba ka tozartashi ba. Yafi zama alkairi ga mumini ya rufe asirin Dan uwansa, akan tona asirin sa. 

Domin dukkan mu masu laifi ne, Allah ne yake rufa namu asirin. “Allah ya kiyaye mu daga dukkan masifa da sharrin kanmu dana Shaidan. Yana da kyau mu san abokin Mu’amala, ba kowa ne ke zaune da kai saboda Allah ba. Mai Aiken sharri domin tozarta wani. YA BAR KOFAR SA A BUDE.” 

A bangarensa Ali Nuhu ya rubuta: “Ya Allah babu wani abu mai sauki face wanda ka saukaka, ina rokon ka da ka saukaka mata a wannan lokaci mafi wahala. Ki kasance mai karfin zuciya ‘yata kuma Allah ka kare mu daga makircin makiya.” Rahama Sadau ta rubuta: “Duk Wanda Ya Tozarta Wani, Allah Zai Tozarta Shi. Allah Ya Isa Abinda Akayiwa Maryam Booth.” 
Dadai sauran masoyanta wadda basuji dadin wannan abinda ya faru ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button