Uncategorized

Mahaifiyata Ba Ta Yarda Ina Murza Leda A Turai Ba Har Sai Da Ta Gan Ni A Talabijin – Sadio Mane 

Mahaifiyata Ba Ta Yarda Ina Murza Leda A Turai Ba Har Sai Da Ta Gan Ni A Talabijin – Sadio Mane 

Mahaifiyar Sadio Mane ba ta gama amincewa da cewa gaskiya ne ɗanta na murza leda a Turai ba har sai da ta gan shi da idanuwanta a cikin talabijin. Sam ba ta yarda da maganarsa ba a lokacin da ya kira ta a waya ya ce mata yana Turai.

“Ba zan taɓa mantawa ba da ranar da na fara zuwa Faransa domin in yi gwaje-gwajen lafiya tare da sanya hannu a kan yarjejeniyar fara kwantiragi da ƙungiyar ƙwallon ƙafar Metz. Ya kamata a ce na fara yin atisaye a ƙungiyar a ranar da na fara zuwa amma kocin ya ce min in zauna a gida.

“Ba ni da kuɗi a wayata da zan iya kiran mahaifiyata domin na gaya mata cewa na tafi ƙasar Faransa. Washegarin ranar na fita tare da wasu abokanaina waɗanda suke wasa a Metz, inda kuma na kira ta na bayyana mata cewa ina Turai.”

“Cikin kiɗimewa ta ce min ba za ta iya amincewa da labarin da nake gaya mata ba. Da dariya na ce mata ina Faransa ta ƙasashen Turai. “Me kake nufi da Turai? Kai da kake zaune a Sanegal. Ya kamata a ce kana tare da kawunka. Na amsa, na ce e haka ne, amma yanzu ina Turai.”

“Mamaki ya mamaye zuciyarta. Abu ne saɓanin tunani! Tsananin mamaki har ya sanya ta dinga kira na a kullum tana tambayar wai shin da gaske nake ina Turai? Sam ba ta yarda ba har sai da wata rana na ce mata ta kunna talabijin domin ta gan ni ina murza leda.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button