Labarai

Magu ya kaucewa tambayar da akai masa kan badakalar Ganduje

Shugaban hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ya EFCC Ibrahim Magu Yaki amsa tambayar da aka yi masa dangane da bakadalar da ya dabaibaye Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje akan zargin da ake masa da karbar na goro a hannun ‘Yan kwangila.
Hukumar dai ta EFCC na shan matsin lamba kan batun na Gwamna Ganduje, shin ko zasu binciki lamarin ko kuwa zasu kawar da kai kamar yadda ake musu zargi a yanzu na yin shakulatun bangaro kan batunsa.
Jaridar Daily Nigerian ce dai ta fallasa wata badakala ta Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a wasu fayafayen bidiyo da ya wallafa inda aka hasko Gwamna na karbar tumuni daga hannun ‘Yan kwangila.
Daily nigerian 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button