Labaran siyasa

MAGANAR GASKIYA ATIKU BAI KYAUTA MA MASOYAN SA DA SAURAN ‘YAN NAJERIYA BA.

MAGANAR GASKIYA ATIKU BAI KYAUTA MA MASOYAN SA DA SAURAN ‘YAN NAJERIYA BA.

Daga Anas Bin Hamza

Naji zafi matuka da ATIKU ABUBAKAR yaki shiga cikin dakin taron mahawara da aka gabatar jiya a dakin taro na Hilton dake garin Abuja domin ya fafata. Duk da cewar ya halarci taron amman shiga cikin dakin taron ne baiyi ba.

Duk da cewar ATIKU ya bada uzurin sa na kin fafatawa a mahawarar, amman wannan bai isa ya zama dalilin sa nakin shiga mahawarar ba.

Dalilina kuwa shine:
Akwai milyoyin masoya ATIKU da suke ta jiran wannan rana domin suga irin abubuwa da kudurin da yake dasu ga kasa da kuma ‘yan kasa baki daya domin yazo ya gabatar mana dasu mu gani kuma muji sannan mu shaida. amman kwatsam SAI ya ki shiga ciki yayi tafiyar sa wai saboda Shugaban kasa Muhammad Buhari bai halarci taron ba.

Ai inace taro ne da aka tsara domin kowane dan takaran shugaban kasa guda BIYAR da aka za6a acikin 76 da suzo su fadawa duniya da kuma talakawan najeriya shirin su da kuma kudurin su ga kasar baki daya. Ba wai ankirkiri mahawarar bane don kawai ATIKU ya kalubalanci BUHARI, ko kuma BUHARI ya kalubalanci ATIKU. Ko kadan ba don haka aka tsara abun ba sai de don kowanen su yazo ya Fada mana kyawawan shirin sa a gare mu tare da ansa tambayoyin wasu daga cikin masu sauraro.

Wannan abun kunya ne a gare su duka biyun ATIKU & BUHARI, hujja kuwa itace: inda ace kowanen su yana kishin kasar da kuma kishin alummar kasar da babu wanda zai ki halarta. Shi baizo ba, kai kuma kaje amman kaki shiga to don me? Musu zakuyi tare ko kuwa fada?

Baku daraja mu ba, sannan baku kyauta mana ba wallahi. Wannan shirin pa ba iya najeriya kawai za’a kalla kuma a saurara ba kadai, duka duniya ana kallo domin aga me kazo dashi amman sai kuka ki saboda kun raina kasar Ku.

ATIKU ABUBAKAR yayi asarar wata dama da lokacin da ya kamata ace ya jawo hankalin dubban masu za6e da basu da za6i, akwai wadanda basu San wa zasu za6a ba a matsayin shugaban kasar su, akwai wadan da suke jiran a gabatar da mahawarar domin suga waye yake da manufa mai kyau acikin su don su za6e shi, akwai wadanda kuma suka raba Kafar su Biyu, daya suna tunani zasu za6i BUHARI, daya kuma suna tunanin zasu za6i ATIKU basu dai da tabbas sai ajiyan ne suke sa rai zasu fidda wanda zasu za6a Amman kashhh sai yaki shiga ciki. Wannan shine babban abunda yafi 6ata mun rai matuka.

Ba Fada bane, mahawarace domin kowa yazo ya fadi kudurin sa, manufar sa, niyyar sa da kuma tsarin sa domin KAWO walwala da jin dadi ga alummar najeriya baki daya. Ta yanda zaka KAWO hanyar da zata kaimu ga tudun mun tsira.

Gaskiya wannan kuskure ne babba da ATIKU ABUBAKAR ya tafka. Duk da cewar kafin yabar gurin sai da yayi jawabi sannan ya baiwa masoyan sa hakuri nakin shiga cikin dakin taron dalilin rashin zuwan BUHARI, to Amman Ni dai gaskiya abun baimun dadi ba, kuma ya Sosa mini raina kwarai da gaske, Amman babu yanda zanyi dole sai de nayi hakuri Dole.

Duk da cewar ina son ATIKU ABUBAKAR har ga Allah to wannan bazai zama hujjar kin Fada masa gaskiya ba, ko kuma gyara masa a lokacin da naga yayi kuskure, hasali ma wannan itace soyayya ta gaskiya….
Allah yasa yaji kuma ya gyara Ameen.

ALLAH YA SA MU DACE.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button