Labaran Duniya

Mafi Karancin Albashi: Kwamitin Zaman Sulhu Ya Kasa Cimma MatsayaKwamitin ‘yan uku da suka hada da wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyoyin kwadago da na masu masana’antu masu zaman kansu, sun kasa cimma matsaya, a zaman tattaunawa da suka yi a tsakanin su, don sulhunta batun tafiya yajin aiki da ‘yan kwadagon suke shirin yi. Shugabar kwamitin, tsohuwar shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Ms Ama Pepple, ce ta shaidawa manema labarai hakan, da yammacin yau Litinin a Abuja. 

Ms Pepple din ta bayyana hakan ne, bayan an kasa cimma daidaito a zaman da akayi na kusan awanni tara, tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyoyin kwadago da na masu masana’antu masu zaman kansu. 

Amma tace kwamitin ya cimma matsayar mika wa shugaban kasa Buhari, bukatar ‘yan kwadagon da kuma ta wakilan gwamnatin tarayya, inda shi kuma zai mika wannan bukatun biyu ga majalisar dattijai don samar da matsaya da kowa zai amince da ita. 

Gwamnatin Tarayya tana fatan ‘yan kwadagon ba zasu tsunduma cikin yajin aiki ba, amma alamu sun nuna, ‘yan kwadagon suna kan bukatar su, na lallai sai sun shiga wannan yajin aiki a gobe Talata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button