Labaran siyasa

LABARI DA DUMI DUMINSA Buhari ya tozarta Gwamna Ganduje a Daura lokacin bukukuwan Sallah

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya watsawa gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje kasa a ido kasa a ido a lokutan shagulgulan bukukuwan Sallah babba da ta gabata kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta Daily Nigerian.
Kamar yadda muka samu daga majiyar tamu, shugaba Buhari ya yi fatali ne da bukatar da gwamnan ya aike masa cewar yana so yazo yayi masa barka da Sallah inda shi kuma Buhari din ya ce baya son duk wani taron siyasa a gidan sa don kuma hutun Sallah yazo.
Buhari ya tozarta Gwamna Ganduje a Daura lokacin bukukuwan Sallah

Buhari ya tozarta Gwamna Ganduje a Daura lokacin bukukuwan Sallah
Lastloaded.ga
 ta samu labarin cewa jami’an tsaron dake gadin shugaban ne dai suka sallami yan aiken Gwamnan daga garin na Daura tun kafin Gwamnan ya taho inda suka fada masu shugaba Buhari yace baya da bukatar ganin Gwamnan.
Haka zalika dai majiyar ta mu ta kuma tabbatar mana da cewa daga nan ne dai kuma sai Gwamnan cikin borin kunya ya canza shawara inda ya ziyarci yayar shugaba Buhari din ya kuma halarci kallon hawan daushe na masarautar garin don kar jama’a su gane akwai matsala.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button