Labaran Duniya

Labari Da Dumi Daminsa: Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma APC

Labari Da Dumi Damin sa

Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC

Ya bayyana cewa zuwan Kwankwaso ya kawo musu matsala a jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP Zuwa APC.

Tabbatar da wannan labari ga jaridar Daily Trust da safen nan, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya bayyana cewa

tsohon gwaman ya yanke shawaran fita daga jam’iyyar ne bayan muhawara tsakaninsa da mabiyansa.

Sule ya kara da cewa babu yadda zai yiwu su cigaba da kasancewa cikin PDP dubi ga irin yadda shugabancin jam’iyyar ta kasa ta karkata kan Kwankwaso sabanin sauran shugabannin PDP a jihar.

Daga Bappah Abubakar

#Mikiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button