Labarai

LABARAI: Kwastan Za Ta Fara Aiki Da Na’urar Binciken Kaya A 2019Kwastan Za Ta Fara Aiki Da Na’urar Binciken Kaya A 2019

Hukumar Kwastan ta Nijeriya ta bayyana shirin ta na fara amfanin da na na’urar zamani don binciken kayyaki a filayen jiragen sama da kuma iyakokin kasar nan, sabon fasahar da ake kira da ‘Electronic Cargo Tracking System’ zai fara aiki ne a shekarar 2019. Shugaban hukumar, Hameed Ali, ne ya bayyana haka a taron manemamlabarai na hadin gwiwa da takwararsa na kasar Uganda, Kateshumbwa Dicksons. Tattaunawar ya biyo bayan, taro da gabatar da jawabai ne da aka yi a makarantar jami’an kwastam ‘Nigeria Customs Command and Staff College’ dake garin Gwagwalada, a yankin Abuja ranar Laraba. Mista Ali ya yi bayanin cewa, hukumar kwastam a karkashin jagorancunsa ta na duba hanyoyi daban daan na zamani don ganin an samu nasarar fara aii da tsarin ‘electronic cargo tracking system’ a fadin kasar nan gaba daya. Ya tabbatar da cewa, za a fara aiki da wannnan tsarin a shekarar 2019, don binciken kayayyaki a dukkan hanyouin shiga fita kasar nan. “Zuwa shekara mai zuwa in har muka samu isassun kudade, kuma kuma cimma yarjejeniya a tsakanimu da kamfain ‘Technology Serbice Probider’ lallai za mu fara amfani da wannan sanon tsarin don lura da kayayyakin dake shigoa gaba daya. “Duk da cewa, muna amfani da irin wannnan fasahar a wasu iyakokin kasar na, muna da bukatar samar da na’urar da zai kula da dukkan aiyyukan da muke yin a lura da kayayyakin dake shigowa kasar nan gaba daya,’’ inji shi. Shugaban hukumar ya kuma kara da cewa, tuni suka kammala sa hannun a yarjejeniya tsakaninsu da abokan aikinsu na kasar Uganda, don a samu nasarar cimma wannna burin. Mista Ali ya bayyana cewa, hukumar kwastam ta Nijeriya da takwararsa na kasar Uganda suna da buri daya a fagen samar da kudaden shiga da kuma kara bunkasa harkokin aiyyukansu. Ya amfani da kimiyya da fasaha wajen harkokin aikin kwastam zai yi matukar taimakawa wajen yaki da fasa kwauri musamman masu shigo da makamai da kuma kungiyouin masu aikata laifuka. Ya ce, tuni suka hada hannu da takwarorinsu na kasar Uganda don ganin yadda za a fara aiki da wannna fasahar a cikin kasar nan. A nasa jawabin, Mista Dicksons, shugaban hukumar Kwastam na kasar Uganda, dole kasashen biyu su hada hannu don warware matsalolin da ke fuskantar hukumomin biyu a ksshensu. Mista Dicksons ya lura da cewa, ayyukan kwastan na Nijeriya da kasar Uganda duk daya ne, a saboda haka a kwai bukatar a hada kai don samun nasara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button