Raayi

KUNGIYAR ALWA SAKE KARRAMA HAJIYA ASIYA BALARABA ABDULLAHI GANDUJE DA LAMBAR YABO KAN AYYUKAN JIN ƘAI

KUNGIYAR ALWA SAKE KARRAMA HAJIYA ASIYA BALARABA ABDULLAHI GANDUJE DA LAMBAR YABO KAN AYYUKAN JIN ƘAI

Daga: Assalafi Isah Ibrahim

A cikin ƙasa da ƴan kwanaki kaɗan da samun lambar yabo daga kamfanin mai na ƙasa (NNPC) a sanadiyyar nasarar lashe wata gasa da kamfanin ya shirya a tsakanin ma’aikatansa a duk ƙasa gaba ɗaya.

Yanzu haka ɗiyar ta mai girma gwamnan Jihar Kano, Hajiya, Asiya Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, (Ƴar Aljannah), “Fulanin Zannan Laisu Of Fika”, ta sake samun wata gagarumar babbar lambar yabon daga wata katafariyar ƙungiyar jagorancin mata ta Nahiyar Afrika gaba ɗaya mai suna “African Leading Women”, (ALWA), ƙarƙashin jagorancin Ambasada, Chris Odey.

(ALWA) ta karrama Hajiya, Asiya  Balaraba Abdullahi Ganduje, (Fulanin Zannan Laisu Of Fika, “Ƴar Aljannah” da wannan gagarumar lambar yabo ne a sanadiyyar yabawa da ƙoƙarin da ta ke yi kan ayyukan jin ƙai da taimakon al’umma da tallafawa marayuwa da gajiyayyu da mabuƙata da kuma tallafawa mata da matasa da ɗumbin al’umma kan harkokin sana’o’i da karatu da kuma rashin lafiya da sauran fannonin ayyukan jin ƙai da gina rayuwar al’umma.

Daga cikin mutanen da su ka wakilci Hajiya,  Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, “Fulani Zannan Laisu Of Fika”, (Ƴar Aljannah) wajen karɓo wannan lambar yabo sun haɗa da:

-Hajiya Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a
-Dakta Habibu
-Onarabul Farouƙ Sulen Garo
-Hajiya Habiba Mamee
-Hajiya Nafisa Umar
-Onarabul Alin Madu
-Onarabul Musbahu
-Onarabul Abdul’aziz
-Onarabul Adamu Ali
-Onarabul  Tijjani.

Waɗanda mafi yawansu tsoffin mataimaka ne na musamman ga mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Ko shakka babu, wannan gagarumar nasara ce ga mai girma Hajiya, Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje da al’ummar wannan Jihar gaba ɗaya, duba da yadda hasken tauraruwar tata ya gama mamaye cikin gida Nageriya ya kuma haura har zuwa sassan Nahiyarmu ta Afrika gaba ɗaya, duk a sanadiyyar kyawawan halayenta da kuma ɗabi’unta na taimakawa al’umma a kowane lokaci.

Haƙiƙa ba abin mamaki ba ne sannu a hankali Duniya gaba ɗaya ta cigaba da girmama Hajiya  Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje kan waɗannan kyawawan halaye nata ga rayuwar al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button