Kiwon Lafiya

Kuna wanke hannu da sabulu idan kun yi ba-haya?

Binciken masana kiwon lafiya ya ce yawancin al’umma ba su damu da muhimmacin tsaftar hannu ba don kariya daga kamuwa da cututtukan da kazantar hannu ke haifar wa.


Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 15 ga watan Oktoba a matsayin ranar tsaftar hannu ta duniya.
Taken bikin bana shi ne “tsabtace hannu – ginshikin kiwon lafiyar al’umma.”
Masana kiwon lafiya sun ce wajibi ne jama’a su dauki dabi’ar wanke hannu da muhimmanci domin rage mace-mace sakamakon cututtukan da kazanta ke haifarwa.
Kungiyar WaterAid mai rajin samar da tsaftataccen ruwa a duniya ta ce wanke hannu da sabulu na iya magance kamuwa cutar amai da gudawa da kusan kashi 50.
Amma kungiyar ta ce kashi 19 ne kawai a duniya suka damu da wanke hannu da sabulu musamman idan sun yi bayan-gida.
Rahoton kungiyar ya ce mutum daya cikin biyar ne ke wanke hannu bayan kamala bayan-gida.
WaterAid ta ce a Najeriya kimanin mutane miliyan 157, kusan kasha 13 na ‘yan kasar ba su samun isa ga abubuwan da za su wanke hannu da su, kuma matsalar ta fi Kamari a karkara da kuma masu karamin karfi a birane.
Sannan an bayyana cewa matsalar ta fi shafar yara kanana wandanda ke mutuwa sakamakon cututtuka da ake samu daga rashin tsaftar hannu.
A ranar wanke hannu ta duniya, WaterAid ta bukaci gwamnatocin duniya da su karfafa wayar da kan jama’a kan muhimmacin wanke hannu da kula da tsafta domin ceton rayuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button