Labarai

Kotu ta bada belin Fayose akan kudi Naira miliyan 50

Babbar kotun tarayya dake birnin Ikko a jihar Legas ta bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose akan kudi Naira miliyan 50.

Haka kuma, kotun ta nemi Fayose ya gabatar da mutane biyu da suka mallaki gidaje a Legas domin su tsaya masa.

Huiumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ce dai ta gabatar da tsohon Gwamnan gaban kotu kan zargin badakalar kudade.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button