Labaran siyasa

Ko Kun San Abin Da Buhari Ya Fadawa Sakkwatawa?

Tawagar yakin neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta isa jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar a Ranar Laraba, a ci gaba da neman kuri’u da shugaban yake yi na neman shugabanci na biyu.
Ga kadan daga cikin abin da ya fadawa al’umar jihar Sakoto kamar yadda wakilin jaridar voa_hausa ya rawaito Muratala Faruk Sanyinna ya aiko mana da rahoto:
Boko Haram: “Cikin ikon Allah, ku ne shaidu, mun yi iyakar kokarinmu, kuma a jiya, mutanen Borno sun tabbata mun ci karfin Boko Haram.
Noma: “Batun arzikin kasa da wadata, Allah ya taimake mu, damunoni biyu da suka wuce, sun yi albarka.”
Cin Hanci Da Rashawa: “Batun cin hanci da rashawa, wannan gwamnatin tana kokari akan ka’idodin da aka kafa. Na yi muku alkawarin, ni ba zan ci amanarku ba, ba kuma zan ga ana cin amanarku ba in kyale.”
Yayin nasa jawabin, Ministan sufuri kuma shugaban gangamin yakin neman zaben shugaba Buhari, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin za a gina layin dogo da zai hade yankunan jihohin Sakoto, Kebbi da Zamfara.
Source: voahausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button