Labaran wasanni

Ko Ka San Abin Da Pogba Yayi Tun Bayan Korar MourinhoTun lokacin da sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester wato Ole Gunnar Solskjaer ya karbi ragamar kungiyar basuyi kunnen doki ba ballantana rashin nasara. Sai dai a wannan al’amari dan wasa Poul Pogba shine yake kai gwauro ya kawo mari domin farfado da kungiyar ta Manchester United daga dogon suman da tayi na rashin samun nasara a lokacin Mourinho. 

Daga wasanni 3 da suka fafata tun bayan zuwan mai horas war ga irin bajintar da Paul Pogba yayi: Pogba ne dan wasan da yafi zura kwallaye a raga. Pogba ne dan wasan da yafi taimakawa a zura kwallaye. Pogba ne dan wasan da yafi buga kwallo da karfi.

Pogba ne dan wasan da yafi kai munanen hare-hare. Pogba ne dan wasan da yafi kowa tava kwallo. Pogba ne dan wasan da yafi kowa kirkirar damarmaki a wasannin nasu guda 3 da suka buga. 

Shin rashin nasarar Manchester United ta baya akwai laifin tsohon mai horarwa wato Mourinho? Ko kuwa shine baisan yadda zai tafiyar da ‘yan wasansa ba? “Pogba babban dan wasa ne wanda zai taimakamin sosai wajen ganin mun kawo karshen halin da kungiyar nan ta shiga na rashin samun nasara a wasanni kuma nasanshi tun yana matashin dan wasa” in ji Solkjaer Ya ci gaba da cewa “Babban dan wasa ne saboda haka bazan koya masa komai ba amma zan gaya masa irin abin da yakamata ya dinga bugawa kuma yanason cin kwallaye hakan yasa nabashi damar zuwa wajen cin kwallon.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button