Labarai

Kisan kai: ‘Yan sanda na neman Salisu Sagir Takai

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na neman Salihu Sagir Takai dan takarar mukamin gwamna a karkashin jam’iyyar PDP da ya kai kansa ofishinsu ranar Litinin 15 ga watan Oktoba domin kare kansa daga zargin kisan wani dattijo mai shekara 70.
Sanarwar da kakakin rundunar, Sufritenda Magaji Musa Majiya ya sanyawa hannu a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabi’u Yusuf.
Sanarwar ‘yan sanda ta ce a ranar Asabar 13 ga watan Oktoba dan takarar gwamnan ya fito daga filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano akan hanyarsa ta zuwa gidansa tare da wasu magoya bayansa.
Magoya bayan da ke cikin tawagarsa sun sari wani dattijo mai shekara 70 da haihuwa a ka a daidai shataletalen Ahmadu Bello Way, lamarin da yayi sanadin mutuwarsa.
Sanarwar da ‘yan sanda ta kuma ce magoya bayan Salihu Sagir Takai sun rika barnata dukkan allunan talla na ‘yan takara masu adawa da shi a kan hanyarsu ta zuwa gidan nasa.
Sun kuma rika cin mutuncin al’ummar da suka hadu ta ita.
Sanarwar ta ce da wadannan dalilan ya zama wajibi ta kira dan takarar da ya bayyana mata dalilin da magoya bayansa suka dauki wadannan matakan na kisan kai da tayar da hankalin al’umma da barnata dukiyarsu.
Amma a nasa bangaren, Salihu Sagir Takai ya musanta cewa rundunar ‘yan sanda jihar ta Kano sun gayyace shi zuwa ofishinsu akan wannan batu.
A wata hira da suka yi da Yusuf Ibrahim Yakasai na BBC, ya ce a shirye yake yaje wurinsu domin kare kansa daga wannan zargin.
Ya kuma musanta cewa magoya bayansa ne suka aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.
Ya kuma yi Alla wadai da wannan abin da ya faru, inda yayi kira da hukumomi su gudanar da cikakken bincike a kan al’amarin domin gano wadanda ke da alhakin wannan aiak-aikar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button