Labarai

Kin ba da hadin-kai a ci amanar kasa ne dalilin cire ni daga TETFUND’

Tsohon shugaban hukumar bayar da tallafi ga manyan makarantu ta Najeriya wato TETFUND, Dokta Baffa Abdullahi Bichi ya yi zargin cewa rashin jituwa ce tsakaninsa da ministan ilimin kasar, Malam Adamu Adamu ta kai ga sauke shi daga mukaminsa.
A wata tattaunawarsa da BBC, Dokta Baffa ya zargi cewa a daren wata Juma’a aka sanar da shi cewa ministan ilimi ya kai takardar kara gaban shugaban kasa inda ya bukaci a soke shi, kuma wannan ba shi ne karon farko da ake samun irin hakan ba.
A cewarsa, yana fuskantar suka sosai a tsawon wata da watanni a gaban shugaban kasa, amma ba wai saba ka’idar aiki ba.
Ya ce ko a lokacin da aka kira shi cikin dare domin sake tabbatar masa cewa za a cire shi daga mukaminsa, sai da ya tambaye laifin me ya yi, amma sai aka ce masa minista ya kai kara a kan sa cewa ”wai ba ya iya samu na, na biyu kuma wai ba na daukan umarninsa na uku kuma wai ina magana da ‘yan jaridu ba tare da sahalewarsa ba.’
Dokta Baffa ya ce shi ministan ilimi ya san cewa samunsa ya fi komai sauki domin kullum suna tare, kusan aiki biyu ma ya ke yi wato aikinsa na hukumar TETFUND da kuma aikin ministan a ma’aikata.
Ya kuma karyata batun cewa ya taba karba kudin kwangila daga makarantun da hukumarsa ke bai wa kudi.
Dokta Baffa ya ce soke shi bai zo masa da mamaki ba domin tsawon shekara guda da rabi da ya yi yana aiki yana cikin matsi saboda wasu ka’idojin minista da ya ke bijirewa. 
Sourec: BBC HAUSA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button