Kiwon Lafiya

Kiba Na Iya Janyo Cutar Kansa -MasanaMasana ilimin kimiyya sun bayyana cewar wani binciken da aka yi ya nuna cewar mutane masu kiba, suna iya kamuwa da cutar kansa. 
Kamar dai yadda kafar sadarwa ta tashar watsa labarai ta BBC ta bayyana masana ilimin kimiyya daga kwalejin Trinity dake Dublin, jamhuriyyar Ireland sun gano cewar da akwai wata kwayar halitta, wadda jiki yake amfani da ita, wajen `zamewa sanadin toshewar wani wuri wanda kuma saboda kitse ne sai abin kuma ya daina yin wani aiki. 
A kasar Nijeriya yadda ake samun shiga cikin al’amari na kiba wadda wasu mutane suke da ita , abin kuma yas fa ne daga kashi 20.3 zuwa kashi 35.1 , ya yin da kuma yadda za a iya samun kiba abin ya fara ne dagab kashi 8.1 zuwa kashi 22.2 kanar dai yadda Hukumar kulawa da bayanai wadanda suka kunshi bayanan al’amuran da suka shafi fasaha ta bayyana. Masana suna ganin cewar shi kitse duk inda yake a jikin mutum ita ko kuma shi suna aikawa da wasu sakonni ne, suna kuma iya kawo barna ga wasu kwayoyin halitta, wanda kuma ta hakan ne za a iya kamuwa da cutar kansa, wadda wasu suka fi sani da ciwon daji. Sai dai kuma wani abin farin cikin wadansu masu ilimin kimiyya daga kwalejin Trinity sun samu wata dama ta nuna wa duniya cewar ta mujallar Nature Immunology yadda kwayoyin halittar jiki suke yaki da cutar kansa kitse ke rufe su .

Daya daga cikin marubutan hadin gwiwar Farfesa Lone Lydia Lynch ta bayyana cewar “A kwai wani sinadari wanda ke rufe kitse wadanda su kwayoyin halittar suke abin yana iya taimakawa. Mun yi kokarin yin hakan cikin dakin gwaji, muka kuma gano cewar hakan na iya basu damar samun nasarar kashe ko kuma toshe kitsen. Amma kuma babbar hanya wadda take mafita ita ce a samu a rage nauyi saboda kuwa hakan shi ne abinda ya fi.” Dokta Leo Carlin wanda yake cibiyar bincike akan cutar kansa dake UK Beatson ya bayyana cewar “ Duk da yake mun san cewar kiba tana taimakawa wajen yiyuwar kamuwa da nau’oin cutar kansa 13, amma har yanzun bamu gane ba sosai yadda da dukkan al’amuran suke faruwa ba. 
“ Wanan nazarin ya bayyana yadda su sinadaran fat suke hana suma wasu kwayoyin halitta wahen sake sake mazaunin shi kumburin, daga nan kuma sai a samu wata hanya wadda za a gane shi maganin da kuma yadda za a yi amfani da shi. “ Da akwai bukatar maida hankalin wajen yin wasu bincike- bincike akan yadda shi kumburin a sanadiyar cutar kansa yake girma, saboda a samu samin yadda al’amarin yake gudana, saboda haka wannan tunatarwa ce mai nuna cewar kamata ya yi mu fara tunanin idan bamu far aba akan kwayoyin halitta wadanda suke taimakwa wajen yaki da abubuwan da zasu iyya cutarwa kamar dai yadda Carlin ya bayyana ”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button