Labarai

KAYI REGISTER YANZU] SABON TSARIN P-YES DA GWAMNATIN TARAYYA TA SAMAR DOMIN SAMARWA MATASA 774,000 AIKIN YI
Kayi Register Yanzu] Sabon Tsarin P-YES Da Gwamnatin Tarayya Ta Samar Domin Samarwa Matasa 774,000 Aikin Yi

Tsarin *Presidential Youth Empowerment Scheme (P-YES)* Sabon tsarin da gwamantin tarayya ta samar mai kama da tsarin *Npower*.

An samar da tsarin karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da kuma ofishin mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan harkokin matasa da kuma dalibai.

An shirya tsarin domin samarwa matasa Dubu Dari Bakwai Da Saba’in Da Hudu ayyukan Yi.

Abubuwan Da Mutum Yake Bukata Domin Neman Wannan Damar:*
1. Ya zama dan Nigeria
2. Daga dan shekaru 18 zuwa 40
3. Ya zama kana iya jin harshen turanci da kuma wani daga yaren da ake amfani dasu a Nigeria
4. Dolene ka cike form na wadanda zasu tsaya maka (Guarantor)
5. Shaidar zama dan karamar hukuma.

*Yadda Ake Neman Wannan Damar Shine”*
1. Zaka shiga shafin da aka samar domin wani yin register wannan tsari wato 


APPLY HERE

2. Idan ba zaka iya cikewa ta nan ba zaka iya zuwa kafa da kafa domin karbar foam din wannan tsarin da zaka cike abubuwa direshi kamar haka:


Ofishin mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan harkokin matasa da dalibai dake hawa na biyar
Federal Secretatiat Complex,
Central Business District,
Abuja, Nigeria
Ko a kira lambobin waya kamar haka:
+234 (0) 803 568 4620
+234 (0) 806 000 0399
+234 (0) 803 460 0766
+234 (0) 806 613 2217

Allah Ya Bada Sa’a Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button