Fadakarwa

KASIDAR ILMANTAR DA DAN KASA MAI KADA KURI’A- AMINU R. TELA

KASIDAR ILMANTAR DA DAN KASA MAI KADA KURI’A….

✍ Aminu Rabiu Tela

Bismillahir Rahmanir Rahim Wasallallahu Alan Nabiyul Kareem…
GABATARWA
2019, wata sheka da za’a sakeyin zabe ta zagayo. Mahimmancin zabe shine ya taimake mu wajan yanke hukunci akan wadanda zasu mulke mu a matakai daban-daban ta hanyar jefa kuri’a.

*ABINDA AKE TSAMMANI DAGA GARENI A MATSAYINA NA DAN KASA MUSULMI*
• Kasan cewa wajibi ne kayi biyayya ga dokokin Allah a kowanne lokaci a cikin komai harma da lokacin zabe.
• Akwai abubuwa da ya zama dole ka kiyaye a matsayinka na dan kasa kuma musulmi a wadannan zabubbuka masu gabatowa.

*WASU ABUBUWAN AKE SO DANKASA KUMA MUSULMI YA AIKATA*
• Fita domin kada kuri’a (A matsayinka na dan kasa na gari)
• Biyayya ga dokokin zabe

• Q 4:59 “Yaku wadanda suka yi imani ku yi da’a ga Allah, kuma kuyi da’a ga Manzonsa, da ma’abota al’amari daga cikinku. Idan kunyi jayayya a cikin wani abu to ku mayar dashi zuwa ga Allah da Manzonsa, idan kun kasance kunyi imani da Allah da ranar lahira. wannan ne mafi alheri kua mafi kyau ga fassara”.
• Ka tabbatar ka kada quri’arka bisa lamirinka. Ka yanke hukunci akan wanda zuciyarka ta nutsu dashi kuma kake ganin zai iya kaika ga chi wajan kwankwadar romin damokradiyya.
• Ka karanci kowanne dan takarada kyau kafin lokacin zabe, kada kayi zabe bisa son zuciya ko son rai, ka zabi wanda kake tunanin zai taimakawa jama’a kuma ya inganta rayuwar mafi rinjaye yan Najeria.

• Q 4:135 “Ya ku wadanda suka yi imani ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa Mahaifanku da mafi kusantar zumunta, ko (Wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci to Allah ne mafi cancanta da al’amarinsu, saboda haka kada ku bi son zuciya harku karkata, kuma idan kuka karkatar da magana ko kuwa kuka kauda kai to lalle ne Allah ya kasance masani ga abinda kuke aikatawa.

• Ka girmama hakkin sauran masu kada kuri’a don su zabi wadanda sukeso ko da ba dan takararku daya ba. Taka rawa acikin tsare-tsaren siyasa haki ne kuma wajibi ne dukkan wanda shekarunsa suka kai na zabe daga dukkanin Addinai ko Kabilu.

• Q 49:13 ” Ya ku mutane! lallai ne mun halicceku daga namiji da mace kuma muka sanya ku dangogi da kabilu domin kusan juna. lalle mafificin daraja a wurin Allah (Shine) wanda yake mafificin takawa, lalle (ne) Allah masani ne kuma me kididdiguwa”.
• Ka fita da wuri domin kada kuri’a da zarar anfara
• Ka kyautata mu’amalar ka da ma’aikatan zabe don sanin yanda zaben zai gudana.
• Kada kaje filin zabe ba tare da katin zaben ka na dindindin ba.
• Zabar dan takara a cikin sirri
• Ka jira har sai an kirga kuri’u kuma ka kiyaye sakamakon da jami’an zabe suka sanar ko suka lika.
• Ka zamo me yarda da dukkan wani sakamako wanda ka tabbatar anyishi cikin adalchi

• Q 3:26 “Kace ya Allah mamallakin mulki, kana bayar da mulki ga wanda kake so, kana zare mulki daga wanda ka ke so, kuma kana buwayar da wanda ka ke so, kuma kana kaskantar da wanda ka ke so, da hannunka alheri yake. lalle ne Kai, a koqanne abu mai iko ne”.

WASU DAGA CIKIN ABUBUWAN DA BA’ASO KA AIKATA
• Kar ka ki fitowa kada kuri’a saboda wasu dalilai mara sa dogaro.
• Kada kaji tsoro ko shakkar magoya baya ko kuma wani dan siyasa.
• Q 9:51 “Ka ce” Babu abinda  yake samun mu face abinda Allah ya rubuta saboda mu, Shi ne majibincinmu. kuma ga Allah, sai muminai su dogara”.

kar ka karbi kudi daga hannun yan siyasa ko kuma sayar da kuri’ar ka da yancinka. ka sani doka bata yarda da saye ko siyarda kuri’a ba saboda cin hanci ne da magudin zabe.

• Q 2:188 “Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadu da ita zuwa ga mahukunta, domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi, ku sani.”

Q:  4:58 “Lalle ne Allah yana bamu unarni da ku bayar da amana zuwa ga masu su (Amanar). Kuma idan kunyi hukunci a tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci. Lalle ne, (Allah) madalla da abinda yake yi muku wa’azi da shi. Lalle ne Allah ya kasance Mai ji ne, Mai gani.”

• Kar ka yada sakamakon karya, kuma kada ka wanzar da kiyayya akan wadanda akan wadanda ba addiniku ko kabilar ku daya ba.

• Q 5:8 “Ya ku wadanda suka yi imani! ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. kuma kada kiyayya da wasu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. ku yi adalci shine mafi kusa da takawa. Lalle Allah masani ne ga abin da kuke aikatawa.

• Ka da ka bari ayi amfani da kai a matsayin dan bangar siyasa domin kai hare-hare  da tashin hankali akan mutane.

• Q 49:6 “Ya ku wadanda suka yi imani! idan fasiki yq zo muku da wani babban al’amari to ku nemi bayani, domin kada ku cuci wasu mutane a cikin jahilci, saboda haka ku wayi gari akan abinda kuka aikata kuna masu nadama.”

 Daga karshe Muna rokon Allah ya bamu damar zabar shugabanni na gari, ya kuma basu ikon inganta rayuwarmu. Ga lambobin sakon karta-kwana don tura rahoto ko sako, ga lambobin kamar haka:
08166662222
08120006622
ga kuma lambobin kira:
07006662222, 07041064855 
hukumar zabe zata yi kokarin samar da maslaha cikin gaggawa.

Cc: Reclaim naija
       Osiwa
      Community Life Project (CLP)

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button