Labarai

Kashi 30 Na ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Ciwon Hauka – Gwamnatin Tarayya

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta bayyana cewa, kashi 20 zuwa 30 na ‘yan Nijeriya suna fama da ciwon hauka. Sakadaran dundundun na ma’aikatan Abdulaziz Abdullahi shi ne ya bayyana haka a wajen wani taro wanda ya gudana a garin Abuja ranar Litinin.

 Abdullahi ya kara da cewa, a cikin yawan mutane miliyan 200 da Nijeriya take da shi, ‘yan Nijeriya miliyan 60 ke fama da ciwon hauka. Nijeriya ce ke da yawan masu fama da ciwon hauka.

Ya ci gaba da cewa,“akwai ciwon hauka daban-daban da kuma yadda ake gabatar da shi. Yawanci dai ciwon haukan sun rabu ne kamar haka; mahaukacin tunani, rashin fahimta, haushi, hali da kuma yana yin zamantakewan mutum da sauran mutane.

“A Nijeriya, an kiyasta cewa kashi 20 zuwa kashi 30 na mutane suna fama da ciwon hauka. Wannan lambar tana da matukar muhinmanci ida ka kwatanda da yawan ‘yan Nijeriya wanda aka kimanta sun kai sama da miliyan 200. Abun haushin dai shi ne, kulawan da ake baiwa ciwon hauka a Nijeriya ya yi kadan. Hakama yana yin yadda ake wayarwa da mutanan Nijeriya kai game da ciwon haukan ya yi karanci, domin mun kasa yin tunani a kan matsalar.”
Da yake magana a kan lamarin, jami’in kiwon lafiya Dakta Ebelyn Ngige ya bayyana cewa, ciwon hauka yana damun mutane fiye da ciwon HIB, ciwon zuciya, hatsari da dai sauran su. Ngige ya kara da cewa,“a cikin Nijeriya, kashi 20 zuwa kashi na mutane suna fama da ciwon hauka, wannan yana da matukar muhimmanci sosai. Ya kamata mu kara yin tunani a kan halin da muke ciki na ciwon hauka a wannan kasa.”
Jami’in ya kuma bayyana cewa, kwamitin duba ciwon hauka ya kasa cin nasara ne saboda rashin isassun kudade.

Source: leadershipyau

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button