LabaraiLabaran Duniya

Karin Haske kan daukar Sababbin ma’aikata N-POWER BATCH C 26/06/2020- Kano N-Power President

Karin Haske kan daukar Sababbin ma’aikata N-POWER BATCH C 26/06/2020. – Kano N-Power President

Shin mai shaidar kwalin secondary ( SSCE ) zai iya nema?

Amsa itace Naam zai iya nema.

Ga yadda tsarukan suke :

N-power shirine na Gwamnatin tarayya Wanda ake daukar mabukata masu shaidar karatu tun daga matakin Primary zuwa abinda kake dashi  Kuma sukeda Asusun ajiya na Banki tare da Lambar waya Mai rigista.

Raba-raben Npower

1- N-power Teach ( Malaman Makarantu )
2- N-power agro  ( Ma’aikatan Gona )
3- N-power Health ( Ma’aikatan Lafiya )
4- N-power Build ( Masu aikin gini )
5- N-power Tax ( Ma’aikatan Haraji )
6- N-power Community

1- N-power Teach ( Malaman Makaranta ).
Ana tura masu wannan bangare makarantun gwamnati da Kuma makarantun Hadaka (Community School) Primary, Secondary da Tsangayoyi.
Wannan tsarin suna bukatar masu kwalin NCE, Diploma, HND, ko  degree tareda Shaidar NYSC.

2. N-power Agro: ( Ma’aikatan Gona )
Ana tura masu wannan bangare hukumar Knarda wacce itace take da hakki akan kulawa dasu.

Wannan tsarin ana bukatar masu shaidar kwalin Diploma, HND da Degree, kuma wanda suka karanci fandin Agric ko Nutrition sunada kulawa ta musamman.

3- N-power Health
Ana tura masu wannan bangare ma’aikatar lafiya ta jaha domin su suke da hakkin kulawa dasu.
Wannan tsarin suna bukatar masu shaidar kwalin Certificate, Diploma, HND da Degree.
Daga cikin wadanda suke bukata akwai:

– Midwives
– Nursing
– Medical Record
– CHO, CHEW, JCHEW
– PHARMACY
– Biochemistry
– Health education
Da sauran karatun da yakeda alaka da harkar lafiya.

4.N-power Tax
Wannan bangaren kulawarsu tana zuwane daga Abuja watau ana turo musu da posting dinsu ne bayan tantancewa ta musamman.

A wannan bangaran kuma suna bukatar masu shaidar kwalin HND da Degree ne kaɗai, Kuma wanda suka karanci fannin Finance, Economic, ko Accounting.

5- N-power Build
Wannan bangare ne Wanda ake koyarda harkar gine-gine Wanda yasha banban da ragowar su suna samun horone akan harkar su na tsawan watanni 9 ko abinda yafi haka Kuma ana basu kulawane a makarantun da ake irin wannan karatu ( Technical College ) Wanda daga baya za’a yayesu sai a basu kayan aiki da abinda Gwamnati tayi tanaji akai.

Wannan tsarin suna buƙatar masu shaidar karatun SSCE, Diploma, HND da Degree, bugu da kari wanda bashi da takardan shaidar karatu ma zai iya cikewa.

6- N-Power Community wannan bangaran a shekara ta 2016 an hadesu ne tareda wadanda suke harkar koyarwa don haka idan wannan Karan ma sun samu to sai yadda tsarinsu ya nuna.
Ana iya samun sauyi ko Kuma Kari a wannan raba-raben a wannan Karan 2020.

ABUBUWA MASU ANFANI

1. Bank details: Yazamanto Mai neman wannan shiri yanada asusun Banki Mai anfani tareda lambar BVN Wanda sunansi yayi dai dai da sunan jikin takardin shi na karatu.

2. Email & Phone number: lallai yanada kyau Mutun yazamanto yanada Email Mai anfani Kuma yanada lamabar waya Mai register.

3. Adireshin inda kake zaune da Kuma Adireshin inda aka haifeka yanada ban-banci yana da kyau a kiyaye saboda gudun kada a turaka inda ba anan kake da zama bah yanzu.

4. Ziyartar Shafuka masu anfani na Social Media domin samun bayanai a kowani lokaci.

5. N-Power bata kudi bace kada wani/wata ko wasu suce maka ka bada kudi su samar maka wannan shiri duk girman su da kusancin su lallai a sani cewa shiga wannan shiri kyauta ne. Ka/Ki kiyaye mutuncinka da Mutuncin ki kada wani ya yaudare ko Kuma ya cutar dakai.

6. Abinda ka samu dama Allah ya rubuta rabanka a tare dashi abinda Kuma baka samu bah babu Alkhairi ne fareka.

Assalafi Isa Ibrahim
N-power President Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button