Labarai

KANO: GWAMNATIN JIHAR KANO TA SHIRYA LAUYOYI NA MUSAMMAN DOMIN BIN KADIN YARAN DA AKA SACE A KOTU

KANO: GWAMNATIN JIHAR KANO TA SHIRYA LAUYOYI NA MUSAMMAN DOMIN BIN KADIN YARAN DA AKA SACE A KOTU 
Tun bayan da ya samu labarin wannan mummunan al’amari na sace yara tare da maida su bayi, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bai samu sukuni ba saboda yadda ya shiga cikin damuwa da jimamin wannan mummunan al’amari.
Hakan ne ma ya sanya mai girma gwamna ya tuntuɓi mai girma Shugaban ƙasar Nageriya, Mallam Muhammadu Buhari a wayar salula domin ganin gwamnatin tarayya ta shiga cikin al’amarin an tabbatar da hukunci mai tsanani ga waɗanda su ka aikata wannan al’amari tare kuma da gudanar da binciken ƙwaƙwaf wajen gano masu aikata irin wannan aiki a ko’ina cikin faɗin Nageriya.
A kuma wani mataki na rarrashin iyayen gami da nuna musu kulawar gwamnati, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai kuma gana da iyayen da aka satar musu yaran gami kuma da duba iyuwar kulawa da yaran har zuwa lokacin da za su dawo hankalinsu duba da yadda aka sauya musu addini da tunani a ya yin da aka sace sun.
Haka zalika, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma shirya lauyoyi na musamman domin ganin sun tunkari wannan batu a gaban shari’a har zuwa lokacin da za a tabbatar da hukunci na adalci wajen bin haƙƙin waɗannan yara.
Mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Umar Ganduje bai tsaya a iya nan ba, ya kuma sake tattaunawa da gwamnan Jihar Anambra Jihar da acan ne aka sayar da yaran domin ganin gwamnatin Jihar ta ƙara ƙaimi wajen sanya ido kan masu aikata aiki irin wannan dan ganin an magance su cikin hanzari. Sannan kuma gwamna Ganduje zai gabatar da ƙuduri na musamman a kan wannan al’amari nan gaba a gaban ƙungiyar gwamnoni ta ƙasa (NGF) saboda a samo bakin zaren magance wannan matsala a kowacce Jiha.
Idan jama’a ba su mance ba, ko a jiya sai da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa jami’an tsaro kan wannan nasara ta gano yaran sannan kuma ya ƙara da jan hankalin iyaye da su ƙara himma wajen kulawa da abubuwan da ke faruwa a kewaye da su. Daɗi da ƙari, mai girma gwamna ya ƙara da ba da tabbacin gwamnatinsa wajen ba da dukkan wani haɗin kai da goyon baya ga jami’an tsaro domin cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button