Labari da dumi-dumi

KANO: Ganduje zai cigaba da tafiya da wasu aga tsofaffin Kwamishinoninsa

KANO: Ganduje zai cigaba da tafiya da wasu aga tsofaffin Kwamishinoninsa
Bayan shafe makonni ana ta yada jita-jita, Gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya fidda sunayen kwamishinonin sa. 
Jaridar Platinum Post ta fidda rahoton cewa cikin kwamishinonin da sunayen su suka bayyana cikin Takardar sun hada da tsofin kwamishinoni kamar na Ma’aikatar kula da kananan hukumomi Murtala Sule Garo wanda aka fi sani da “Commander”, da na Ma’aikatar sadarwa, Malam Muhammad Garba, da na Ma’aikatar sharia, Ibrahim Mukhtar, Kiwon Lafiya,  Dr. Kabir Getso, da na ma’aikatar kula da masana’antu Ahmed Rabiu. 
Har ila yau Ganduje ya rike wasu daga cikin tsaffin kwamishinoni na lokacin Malam Ibrahim Shekarau a bangaren Ma’aikatun Kasafi da tsare-tsare, Shehu Na’Allah da Musa Iliyasu Kwankwaso wanda shine tsohon kwamishinan Ma’aikatar Raya karkara. 
Wata majiya mai karfi daga hukumar tsaro tayi nuni da cewa tuni ma har Ganduje ya aika sunayen Kwamishinonin zuwa ga Jami’an tsaro domin tantance su. 
Wanda ya bayyana haka da bai so a bayyana sunan sa ba yace tuni ma har hukumar tsaro ta kammala binciken asali, inda kuma za’a soma tantancewa na ainihi gobe Litinin 14 ga watan Oktoba 2019. 
Za’ayi binciken ne kashi kashi daga ranar litinin zuwa Laraba. 
Majiyar tace zantuka sun yadu sosai a fadin jihar Kano kan yaushe ne Ganduje zai nada kwamishinoni tun bayan rantsar da shi karo na biyu ranar 29 ga watan Mayu 2019.
A wata majiya daga Fadar Gwamnatin jihar Kano kuwa an samu labarin cewa Ganduje zai nada kwamishinoni da zarar an kammala shari’ar sa ta bayan zabe. 
Don haka za’a yiwa kwamishinonin bincike kan abin da ya shafi shaye-shaye a gaban jami’an tsaro na farin kaya da na hukumar Yaki da shan miyagun kwayoyi (NDLEA). 
Sai dai kuma da aka tuntubi jami’in yada labarai na fadar Gwamnatin jihar Kano Abba Anwar yace bai da masaniya akan hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button