Labarai

KANO: GANDUJE YA BIYAWA DALIBAN DAKE KARATU A MAKARANTUN GWAMNATI KUDIN JARABAWAR NECO

 GANDUJE YA BIYAWA DALIBAN DAKE KARATU A MAKARANTUN GWAMNATI KUDIN JARABAWAR NECO

 ….AN GARGADI SHUGABANNIN MAKARANTUN SAKANDIRE DA CEWA AHIR DIN SU DA KARBAR KO QWANDALA A HANNUN DALIBAI

Gwamanan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya dauki nauyin biyawa Daliban da suka fadi Jarabawar Kwalifayin(Qualifying) a Makarantun Gwamnati Kudin Jarabawar NECO, tare da Jan kunne akan Shugabannin Makarantun da cewa kar su kuskura su karbi ko kwabo a hannun Dalibai..

Kwamishinan yada Labarai, Matasa da Al’adu
 Malam Muhammad Garba Shi ya bayyana haka a Lokacin da yake zantawa da manema Labarai a kano, inda ya Bayyana cewa wannan wani kadan ne daga cikin abun da zai tabbatarwa da iyayen yara cewa Mai girma Gwamna da gaske yake wajan bayar da tallafin kudi dumin karatun ‘ya’yan su.

Ya tabbatar da cewa Gwamnati ta biya Kimanin kudi Naira Miliyan Dari Hudu da Ashirin da Hudu da Dubu Dari Tara da Hamsin da Biyu (N424, 952, 000.00) wanda ya zama an biyawa kowane Dalibi Naira Dubu Goma Sha Daya (N11, 000) acikin dalibai kimanin (38, 632) da zasu zana wannan Jarabawa.

Sanarwar ta kara da cewa Babban burin wannan Gwamnatin shine yin aiki tukuru a harkar Ilimi domin ganin an samu Kyakkyawan Yanayin koyo da koyarwa a harkar Ilimi ga al’umma.

Kwamishinan Ya kara da cewa Gwamnati baza ta ta6a zuba ido tana gani al’ummarta su gaza samun Nagartaccen Ilimi wanda zai amfani al’ummar kano daga kowane matakin karatu ba. 
 
Sanarwar ta Kara Jan kunne dai ga Shugabannin Makarantun Sakandire akan cewa Lallai su guji Karbar kowane irin Kudade kafin Dalibi ya karbi sakamakon Jarabawar shi, yayin da ya bayyana hakan a matsayin wani babban laifi kuma Gwamnati tana nan zata soma bincike don ganin shugabanni basu karbi kudaden daga hannun Daliban ba, kuma duk Hedimastan da aka kama da karbar to kuwa babu makawa zai girbi abun da ya shuka.

 Daga Karshe ya bukaci Iyayen Yara, Masu daukan nauyin su ko masu kula da Karatun su da cewa su tabbatar sun hada hannu da Gwamnati ba domin kawai iya kula da karatun yaran su ba, har da Kokarin basu tarbiyar nagartacciya domin samar da al’umma ta gari.

MALAM MUHAMMAD GARBA
Hon. Commissioner, information, Youth & Culture, Kano State
April 8, 2019

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button