Labarai

Kano: An Gano Wasu Mutane Biyu Namiji Da Mace Basa Motsi Cikin Mota Akan Hanyar Katsina

Daga: Abbas Yakubu Yaura

An gano gawarwaki har da wani fitaccen mai gidan rawa, Steven Ayika da kuma uwargidan sa, Chiamaka Emmanuel a jihar Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da samun gawarwakin mutum biyun da suka rasa rayukansu a cikin wata mota.

DSP Haruna yace, “A ranar 11/23/2021 da misalin karfe 04:50, an samu rahoton cewa an ga wata mota a kan hanyar Katsina dake karamar hukumar Fagge jihar Kano dauke da mutane biyu 2, mace da namiji basa motsi.

Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya tashi tare da umurtar tawagar ‘yan sanda dasu ziyarci wurin da lamarin ya faru.

“Nan take tawagar ta garzaya wurin da lamarin ya faru, sun kuma tarar da wadanda lamarin ya rutsa dasu, Namiji da Mace a cikin kujerar baya ta Motar Siena, nan take aka garzaya dasu Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke birnin Kano, yayin da wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu.

DSP Kiyawa ya bayyana cewa, “A binciken farko, an bayyana sunan marigayin mai suna Steven Ayika, mazaunin Jaba Quarters Kano, yayin da matar da ta rasu itama suka samu bayaninan sunanta da Chiamaka Emmanuel, mai adireshi daya. Sai dai ana cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button