Kannywood

Kannywood: Jaruma Maryam Booth ta kamma NYSC (Hotuna)

Fitaciyar Jarumar fina-finan hausa, Maryam Booth ta kammala hidimar kasa na shekara daya da ya zama wajibi kan duk wani wanda ya kammala digiri ko wani abu mai kama da haka kuma bai wuce shekaru 30 ba.
Jarumar tayi amfani da shafinta na sada zumunta na Instagram ne inda ta taya kanta murna da ma sauran masu yiwa kasa hidimar da suka kammala a watan Oktoba.

Kazalika, ta yi fatan Alheri ga dukkan sauran wanda suka kammala hidimar kasar.
Ga abinda ta rubuta, “Rayuwa itace abinda ke faruwa yayinda mutum ke gefe guda yana wasu tsare-tsarensa. Ina taya dukkan ‘yan yiwa kasa hidima da suka kammala hidimar a yau. Allah ya sanya mana albarka.
Ta kuma sanya hoton ta sanye da kayan yiwa kasa hidimar rike da takardar kammala NYSC din.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button