Siyasa

KANAWA: KAR KU MANTA AIYUKAN ALHERIN BABA GANDUJE.

KANAWA: KAR KU MANTA AIYUKAN ALHERIN BABA GANDUJE.

Ya ku alummar jihar Kano, kar ku zama ma su manta alheri, ku tuna da aiyukan alherin gwamnatin Baba Ganduje, Baba Ganduje na kowa, bawan Allah mai halin dattako.

Ku fito ku zabi Baba Ganduje a ranar 23 ga watan Maris 2019 ranar da za’a gabatar da zaben raba gardama a wasu sassan mazabu da ke wannan jiha tamu mai albarka domin ci gaba da aiyukan more rayuwa da habakar tattalin arzikin jama’ar Kano.

Dattijo, Khadimul-Islam ba za mu manta da tulin alheranka ba kamar:
i. Daukar aikin dubban malaman makarantu tun daga firamare, sakandire  har ya zuwa malaman manyan makarantun gaba da sakandire;

ii. Daukar ‘Yan KAROTA dubu biyu rigis don kula da yamutsin ababan hawa bisa titnunanmu don rage yawan hadura;

iii. Daukar daruruwan ma’aikatan Lafiya;

iv. Karasa aiyukan da aka watsar domin jama’ar Kano kamar babban asibitin Giginyu da na yara dake titin Gidan Zoo;

vi. Karasa aiyukan gadar sama da ta kasa da masu karyar cigaban Kano suka watsar;

vii. Kammala wasu muhimman titunan da a ka watsar a dukanin fadin jiha;

viii. Ya kirkiri Karin gadojin sama da na kasa tare da kamala su cikin wa’adi, ga kuma dimbin titina birni da karkara;

ix. Ga kuma biyan ma’aikata albashi a kan lokaci yayinda wasu jihohi ake bin su bashin watanni;

x. Biyan fansho a kan lokaci tare da kudin  sallama wato garatuti;

xi. Biyan kudin tallafin karatu ga daliban da ke karatu cikin gida da wajen kasar nan.

Domin dorawa bisa wadannan aiyukan alheri da kuma kaucewa fadawa cikin koma baya da shiga cikin tirka-tirka da tashin hankalin siyasa wanda zai janyo asarar wadanan aiyuka da ‘yan amutun siyasa ka iya kawowa karkashin kungiyar shegiyar uwa mai kashe ‘ya’yanta wato Ja’iyyar PDP da bakar akidar darikar KWANKWASIYA akidar da ta bijirar da yaranmu ta lalata tarbiyar matasa, ta koya musu bijirewa iyayensu da rashin ganin manya da malumanmu, ku fito ku zabi UBAN ABBA GANDUJE (Khadimul Islam) ranar 23 Maris, 2019 ranar zaben raba gardama.

Kanawa kar ku yi asarar kuri’arku, Ku zabi Uban Abba Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button