Cuta da Maganin ta

Kana fama da cutar Olsa? Yi amfani da sinadarin ‘yayan kankana don samun waraka

– Bincike da dama sun gudana kan amfani da ‘yayan itatuwa, musamman ma kankana, wajen rage kamuwa da cutar nauyin jiki, ciwon sukari, da ciwon zuciya ko yankewar jiki
– Sai dai, masana kimiyya sun tabbatar da amfanin kankana wajen magance cutar Olsa, wacce kowa ya fi sani da cutar ‘yunwa’
– Ko da aka gwada ‘yayan kankana da maganin ‘Renitidine,’ ya nuna amfanin ‘yayan kankana da ma’auni 4000mg/kg, da cewa za a iya amfani da ‘yayan kankana wajen magance cutar olsa

Kankana, na daya daga cikin ‘yayan itatuwan da suka yi suna a wannan duniya tamu. A yayin da muke jin dadi tare da shaukin shan wannan dan icce, mukan rika mantuwa muna tuya babu albasa, ma’ana, mukan riga shan kankanar ba tare da cin ‘yayan da ke a cikinta ba, ba tare da munsan dumbin magungunan da ke tattare da ‘yayan ba.
Bincike da dama sun gudana kan amfani da ‘yayan itatuwa, musamman ma kankana, wajen rage barazanar kamuwa da cutar nauyin jiki da dai sauran cututtuka da suka hada da ciwon sukari, da ciwon zuciya ko yankewar jiki.

Sai dai, masana kimiyya sun tabbatar da amfanin kankana wajen magance cutar Olsa, wacce kowa ya fi sani da cutar ‘yunwa’. Sun yi amfani da ‘yayan da ke jikin kankanar, inda suka gudanar da bincike mai zurfi akai, ta hanyar gwaji a dakin sarrafa magunguna da gano cututtuka dama hanyoyin magance su, inda suka fara yin gwajin akan beraye.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button