Labarai

JAM’IYYUN SIYASA, DA KUNGIYOYIN MASU ZAMAN KANSU SUN TAYA GWAMNA GANDUJE BISA SAMUN NASARA A KOTU-Hausafinest

JAM’IYYUN SIYASA, DA KUNGIYOYIN MASU ZAMAN KANSU SUN TAYA GWAMNA GANDUJE BISA SAMUN NASARA A KOTU-Hausafinest 
Kwanaki kaɗan bayan da Shugaban tarayyar Nageriya, Jeneral Muhammadu Buhari ya aike da saƙon taya murna ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan nasarar da ya samu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna, yanzu haka sama da jam’iyyun adawa (50) da kuma wasu ɗumbin ƙungiyoyi masu zaman kansu, ƙarƙashin ƙungiyar haɗakar jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ake kira “All Parties and Civil Associations Platform” (APCAP), sun aike da saƙon taya murnarsu ga mai girma gwamna kan wannan nasara da ya samu.
A wata takarda da su ka aiko ranar Juma’a, 4 ga watan Octoba, 2019, mai ɗauke da sa hannun jagororin haɗakar, Chief Benjamin Aturu Dogo da Bello Sanin Kwalla, haɗakar jam’iyyun adawar da muhimman ƙungiyoyin sa kan, sun ba da tabbacin cewa: “Abin da ya faru wata gagarumar nasara ce ga dimockaraɗiyya, kamar yadda mai daraja shugabanmu, Jeneral Muhammadu Buhari ya faɗa”.
Kamar yadda sakataren watsa labarai na mai girma gwamna, Mallam Abba Anwar ya sanar, ƙungiyar ta kuma yi tsokaci da cewa, ɗan takarar jam’iyyar (PDP) da aka kayar, Abba Kabir Yusuf, kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba shi dama ya ɗaukaka ƙara, sai dai ƙungiyar ta bayyana hasashenta da cewa: “a bayyane ta ke ƙwararru masana shari’a sun riga sun gama yin hasashe kan nasarar da za ka samu, dan haka ko ka ɗaukaka ƙara ko kar ka ɗaukaka, babu wata nasara da ta rage maka face ka yi ta jira har zuwa 2023”.
Ƙungiyar ta kuma yi bayanin cewa, a bayyana ta ke a lokacin da jam’iyyar (PDP) ta ke gabatar da shaidu a kotu, ba sai masanin shari’a ba ne kaɗai zai fahimta, kowa ma zai iya gane yadda aka gudanar da zaɓe na gaskiya a Jihar Kano.
Kamar yadda su ka faɗa, wannan hukunci da kotu ta yi, ya isa ya ƙara shaida yadda mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya daƙile dukkan wata matsala daga abokan hamayya, duba da yadda Kano ta kasance cikin kwanciyar hankalin da walwala da kuma zaman lafiya tun bayan bayyana wannan nasara ga gwamna Ganduje.
A kuma wani sashe na takardar, sun yi ishara da cewa, ɗaukaka ƙaran jam’iyyar (PDP) ƙarin rauni ne a gare ta, kuma hakan wata ƴar manuniya ce da ke ƙara tabbatar da rauni da gazawar da jam’iyyar ta (PDP) za ta ƙara fuskanta a babban zaɓen da ke tafe na shekarar (2023).
“Haɗakar mafi yawan jam’iyyun siyasa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu, mun kasance, kuma mun yi aiki tuƙuru a lokacin zaɓen gwamnoni da ya gabata a matsayin masu sanya ido cikin zaɓen, gaba ɗayanmu mu na da ƙwarin gwiwa kan yunƙurin jam’iyyar (PDP) na ɗaukaka ƙara ba komai ba ne face za su ɓatawa kansu lokaci da ƙarar da ƙarfi da kuma kuɗaɗensu a banza, kuma jam’iyyar ta gama rushewa a ƙasa gaba ɗaya musamman ma a Jihar Kano”. Su ka bayyana a cikin takardar.
Sai kuma su ka ƙara da yaba cewa: “Jam’iyyar (APC) ta nuna dattako matuƙa wajen gudanar da shagulgulan murnar wannan nasara da ta samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe. Mu na ba wa ƴan siyasar Nageriya tabbacin cewar Jihar Kano ta kai wani mataki na cigaba wajen nuna ƙwarewa da gogewa a dimokaraɗiyya, domin mun ga cewar babu wata matsala da ta afku a ya yin da mabiya jam’iyyar (APC) su ka gudanar da shagulgulan murnar”.
Daga nan kuma sai su ka ƙara da kira ga dukkan jam’iyyun da su ka yi haɗaka wajen taya mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje murnar samun nasara a kotu da su ƙara ƙaimi wajen cigaba da samar da haɗin kai a tsakaninsu domin su tunkari jam’iyya mai mulki ta (APC) a Jihar Kano da kuma ƙasa gaba ɗaya saboda mulki ya dawo hannunsu.
Daga ƙarshe kuma, sai su ka ƙarƙare da cewa, “mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, duk da kasancewarmu jam’iyyun adawa, amma mun gamsu gwamnatinka ta na tafiya yadda ya kamata a Jihar Kano. Sannan kuma za mu bi hanyar da ka bi domin cigaba da ƙarfafa samar da kykkyawar gwamnati”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button