Labaran siyasa

Jami’in Gwamnatin Ganduje ya caccaki Buhari kan kalamansa ga Ganduje a Faransa

Zulyadaini Sidi Mustapha Karaye Wanda shi ne Mai taimakawa Gwamnan Kano na musamman akan hulda da kungiyoyi masu Zaman kansu, ya yiwa Shugaba Buhari tatas dangane da kalamansa akan Ganduje.
Jami’in ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mutum kara dattako da rashin sanin masoyansa na hakika. A wata hira da aka yi da shi a wani Gidan Radiyo a jihar Kano, Zulyadaini ya yi kaca kaca da Buhari.
Zulyadaini yana maida martani ne kan kalaman da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a kasar Faransa, inda yayi magana akan bidiyo da aka ga Gwamnan Kano na sanya dalar Amirka a cikin babbar riga.
Ya bayyana cewar yadda Ganduje yake yiwa Shugaba Buhari biyayya bai kamata ace ya yiwa Gwamnan haka ba, ya kwance masa zabi a kasuwa.
”San Shugaba Buhari ba mutumin da ya san ya kamata bane, ya bayyanawa duniya rashin iya jagorancinsa, wanda Shugaba irinsu ba haka ya dace ya mu’amalanci mutane ba”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button