Labarai

Jami’an Tsaron Farin Kaya Sun Cafke Wasu Masu Laifi a Jihar Nasarawa

Jami’an Tsaron Farin Kaya Sun Cafke Wasu Masu Laifi a Jihar Nasarawa

  Wasu Jami’an Bada Kariya Ga Fararen Hula Na Civil Defense Wasu Jami’an Bada Kariya Ga Fararen Hula Na Civil Defense Rarraba Dubi ra’ayoyi Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defense a jihar Nasarawa ta yi nasarar cafke wasu mutane dake tafka manyan laifuka, ciki har da wasu da bindigogi a yankin karamar hukumar Toto da ake rikici. WASHINGTON D.C. — Shugaban hukumar Civil Defense a jihar Nasarawa Muhammad Gidado Fari, ya ce sun sami nasarar ne biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu daga jami’ansu. Jami’an sun kama mutane biyu dauke da bindigogi, haka kuma sun kama wasu ‘yan fashi guda biyu da kuma wani da laifin lalata dukiyar gwamnati. Shugaban hukumar yace baki ‘daya wadanda aka Kaman za a gurfanar da su gaban kotu. Wasu daga cikin wadanda aka Kaman sun yiwa Muryar Amurka bayanin laifukan da aka kamasu da yi. Daga can yankin da ake rikici tsakanin kabilar Basa da Ibra a karamar hukumar Toto, mai magana da yawun ‘yan kabilar ta Bassa Usman Gimba, ya ce babbar bukatarsu itace su sami masarauta da zata dakile duk wani rikici tun kafin ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyi. Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura ya yi alkawarin ziyartar yankin don samun hanyar shawo kan rikicin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button