Labaran Duniya

Jami’an gwamnatin kasar Sudan ta kudu sun kai ma Buhari ziyara a Villa (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata 2 ga watan Satumba ya karbi bakoncin wata babbar tawagar manyan jami’an gwamnatin kasar Sudan ta kudu a fadar gwamnatin Najeriya dake babban birnin tarayya Abuja.

A jawabinsa, Buhari ya bayyana ma jami’an Sudan ta kudu cewa a shirya Najeriya take ta taimaka musu wajen samun daidaito a sha’anin siyasarsu da kuma fannin tattalin arzikin kasarsu, kamar yadda kaakakinsa, Femi Adesina ya bayyana. “Mu kammu ba wai muna cikin sauki bane, amma tunda Sudan ta kudu tana neman agajinmu, toh a shirye muke mu taimaketa da duk abinda zamu iya, kuma muna tayata addu’ar samun zaman lafiya mai daurewa.” Inji Buhari.

Haka zalika shugaba Buhari ya shawarci shuwagabannin kasar Sudan ta kudu dasu kasance masu sadaukarwa ga kasarsu har sai kasar ta zauna da kyau cikin daidaito domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ne abu mafi muhimmanci a kasa. “Babu yadda za’a a tafiyar da kasa har sai ka tabbatar da zaman lafiyarta, daga nan ne sai tattalin arziki ya fara tashi, dole ne ka samar da ayyuka ga jama’an kasa, musamman matasa, kuma dole ne ka magance rashawa tare da kulawa a da arzikin kasa. Za muyi iya bakin kokarinmu wajen taimaka muku.” Inji shi. 

Shima a jawabinsa, jagoran tawagar kasar Sudan ta kudu, Gatkuoth ya bayyana ma shugaban kasa Buhari cewa kasashe da dama na sha’awarsa a duk fadin nahiyar Afirka tare da yabawa da kamun ludayinsa, saboda haka ne kungiyar kasashen Afirka ta nada shi jagoran yaki da rashawa. 

Daga karshe Mista Gatkuoth ya tabbatar ma shugaba Buhari cewa kasarsu tana kokarin tabbatar da zamn lafiya tare da daidaita kawunan al’ummarta, amma fa tana bukatar taimako daga Najeriya musamman ta bangaren tsaro, sauya dokokin kasa da kuma gudanar da manyan ayyuka. 


Source: naij.ng

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button