Entertainment

Izzar So: An Bayyana Sunan Daraktan Da Zai Maye Gurbi Marigayi Nura Mustapha

AMINU AL-RAHUZ SHI NE SABON DARAKTAN IZZAR SO.

Tun bayan rasuwar Marigayi Nura Mustapha Waye, mai bada umarni a kayataccen shirin nan mai dogon zango ” Izzar So” makallata Finafinan Hausa, suka zuba ido don ganin waye wanda zai maye gurbin marigayin.

A yanzu haka dai kamfanin “Bakori Tv” mallakin Jarumi Lawan Ahmad, ya maye gurbin marigayin da Aminu Al-Rahuz, a matsayin sabon Daraktan shirin Izzar So.

Tun kafin rasuwar Nura Mustapha Waye, Al-Rahuz shi ne mataimakin mai bada umarni a shirin na Izzar So.

Aminu Al-Rahuz yana daga cikin matasa masu bada umarni a Masana’antar Kannywood, kadan daga cikin Finafinan sa sun hada da: So Dangin Mutuwa, Majanyin Zuciya, Sirrin Zuciya, Kama Da Wane, Taraliya, Tarayya, Feenah, Ruwa Biyu, Tafin Hannu, Kurman So, Laure.

A hoton farko, Al-Rahuz ne tare da Marigayi Nura Mustapha Waye.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button