Labaran Duniya

Ina fuskantar barazana saboda labarin fallasa — Jaafar Jaafar

Mawallafin jaridar nan ta Daily Najeriya wacce ake buga wa a Internet Jaafar Jaafar, ya yi zargin cewa ya fara fuskantar barazana a rayuwarsa saboda labarin da ya buga na zargin cewa yana da wani bidiyo da ya nuna gwamnan jihar Kano ya na karbar cin hancin dala miliyan biyar.
Dan jaridar ya ce, a yanzu haka ala tilas ya sauya wajen zama domin tsira da rayuwarsa da kuma lafiyarsa.
Gwamnatin jihar Kano dai ta ce an yi labarin ne don a bata wa gwamnan jihar suna, kuma tana ma duba yi wuwar daukar matakin shari’a a kan jaridar ta Daily Najeriya da kuma mawallafinta.
A hirarsa da BBC, Jaafar Jaafar, ya ce baya tsoron shari’a domin ya na da hujojji masu karfi da ya dogara da su kafin wallafa wannan labarin.
Dan jaridar ya ce, ya samu hotunan bidiyo sama da goma sha biyar da ke nuna yadda gwamnan ke karbar na goro daga hannu ‘yan kwangila.
Kwararru sun yi bincike a kan bidiyon, sannan kuma sun tabbatar da sahihancinsa ba bu batun sharri ko kage ko kuma siddabarun harkar komfuta, inji Jaafar.
Sai dai dan jaridar ya ce ya jinkirta fitar da bidiyon ne saboda matsaloli na tsaro, ”Nan da dan wani lokaci kadan zan fitar da bidiyon kuma abin da ya sa aka samu tsaiko, so nake na ga na samu wuri na zauna lafiya tare da iyali na”.
Ya ce, ”Akwai jami’ai da suka kirani suka ce mun na yi hankali akwai wasu jami’an gwamnati da ke yunkurin far mun saboda naki yarda a yi sulhu da ni”
Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da zarge-zargen da ke cikin wannan labari, inda ta ce ana yunkurin bata wa gwamnan jihar suna ne kawai.
Sanarwar wacce kwamishinan watsa labaran jihar ta Kano Malam Muhammad Garba, ya sanya wa hannu ta ce labarin bai sa Gwamna Ganduje ya yi ko gezau ba.
Wannan labari dai na ci gaba da jan hankulan mutane musamman ma’abota shafukan sada zumunta da ke wallafa kalamai da ra’ayoyi daban-daban a kai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button