Labarai

ILIMI KYAUTA KUMA WAJIBI A JIHAR KANO: SARKIN KANO MUHAMMAD SUNUSI II, YA BUKACI SAURAN JAHOHI SU YI KOYI DA GWAMNA GANDUJE

ILIMI KYAUTA KUMA WAJIBI A JIHAR KANO: SARKIN KANO MUHAMMAD SUNUSI II, YA BUKACI SAURAN JAHOHI SU YI KOYI DA GWAMNA GANDUJE 
Ya Kuma Bayyana Ƙudurin A Matsayin Wani Mataki Mai Cike Da Hangen Nesa.
Shirin mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na maida ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandire a Jihar Kano, mai martaba sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi Lamiɗo Sunusi, II, ya buƙaci sauran Jihohi da su yi koyi da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje wajen gina rayuwar al’umma.
Sarki Sunusi, ya kuma yabawa gwamna Ganduje kan wannan tunani da ya yi, tare da bayyana hakan da cewa: “alfanu ne mai girma wajen ceto rayuwar al’umma. Na yi imani cewa, wannan tunani ne tabbatacce saboda himmar da ake da ita wajen ceto rayuwar al’ummar Jihar Kano da ma jama’a gaba ɗaya”.
Sarki Sunusi ya bayyana hakan ne a jiya a ya yin da gwamna Ganduje ya karɓi baƙuncinsa a ofishinsa shi da wakilai daga Bankin Zenith, waɗanda shugaban Bankin na shiyar Arewa maso yamma, Dakta, Sani Yahaya wanda ya samu wakilcin manajan daraktansa, inda su ka zo domin taya murna ga mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da nasara da ya samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe tare kuma da ba shi tabbacin haɗa gwiwa da gwamnatinsa wajen aiwatar da shirin ilimi kyauta kuma wajibi.
Sarki sunusi, ya ƙara yin tsokaci da cewa: “wannan shi ne haƙiƙanin abin da wannan ƙasa ta ke buƙata. A fada mu na da buƙatar himma sosai domin cimma wannan buri. Saboda Ilimi shi ne ginshiƙin kowacce irin al’umma”.
Abin da gwamna ya ke yi, a cewar sarkin na Kano, “abin misali ne wanda ya tabbata, wanda kuma dama shi ne zai taimaka wajen gina al’ummarmu, kuma akwai buƙatar sauran Jihohi su yi koyi da shugabanci nagari abin misali daga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje”. Inji Sarki Sunusi.
Tare kuma da ƙarawa da cewa, wannan muhimmin al’amari ne ga kowa, akwai buƙatar haɗin kai na gaba ɗaya a taimaka a wannan fanni domin cimma nasarar cigaba mai ɗorewa a sashen ilimi wanda zai haifar da cigaba na bai ɗaya a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Da ya ke nanata matsayar da gwamna Ganduje ya ke kai, gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen ganin cewa al’umma sun zame masu amfani da amfanarwa a madadin su zama nauyi da lalura, shi ma sarki Sunusi ya hau kan wannan matsaya inda ya ke cewa: “aniyar gwamna Ganduje za ta taimaka mana wajen canza al’ummarmu daga matsala zuwa masu amfani da amfanarwa”.
Tun da farko da ya ke tsokaci game da jawaban wakilan Bankin na Zenith, gwamna Ganduje ya bayyana cewa babu wani kewaye-kewaye wajen tabbatar da ilimi mai inganci, “akwai buƙatar mu haɗa hannu gaba ɗaya. Domin ilimi wajibi ne, ya zama lallai mu yi iya bakin ƙoƙarinmu wajen inganta shi”. Inji Gwamna Ganduje.
Bayan da ya gabatar da saƙon taya murna ga mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje Jami’in da ya wakilci shugaban Bankin na Zenith, Mallam Yahaya, ya ƙara da cewa “mai girma gwamna, Bankin Zenith zai kasance wajen ƙarfafar tsarinka na bayar da Ilimi kyauta kuma wajibi tun daga firamare har zuwa babbar sakandirr”.
“Bugu da ƙari, tsarin zamanantar da karatun allo gagarumin al’amari ne na cigaba, akwai kuma buƙatar haɗa hannu tare. Mai girma gwamna mu na matuƙar alfahari da kai”.
Daga ƙarshe kuma sai ya ƙarƙare da cewa, a kowane lokaci Bankinsu a shirye ya ke ya haɗa hannu da Jihar Kano wajen bunƙasa harkar Ilimi, tare kuma da gabatar da cewa: “Waɗannan wasu littattafai ne waɗanda za a iya amfani da su a makarantun firamare da sakandire na wannan Jiha”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button