Labaran Duniya

Hukuncin Daurin Rai Da Rai Ga Duk Wanda Ya Yi Wa Kananan Yara Fyade a Jihar Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta amince da wasu dokoki masu tsanani, ciki har da daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin fyade ga kananan yara.
WASHINGTON D.C. — 

Gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam, ya ce batun fyade da kuma Madigo, na neman zama ruwan dare a jihar don haka ne suka ga ya dace su dauki mataki, na kafa dokoki masu tsanani.
A cewar gwamnan duk wani mutum da aka kama yana lalata da wani yaro da bai balaga ba, hukuncin daurin rai da rai ne. haka kuma duk wani da aka kama yayiwa wata mace fyade da karfi, zai fuskancin hukuncin daurin shekaru 25 a gidan Yari.
Gwamnan ya nuna damuwarsa da labarin da ake samu, na cewa wasu na lalata kananan yara da basu mallaki hankalinsu ba, hakane ya janyo hankalinsu wajen samar da irin wannan doka mai tsanani don magance faruwar hakan a jihar.
Haka kuma an kafa dokar duk wani da aka kama a jihar yana Luwadi, zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 25 shima a gidan Yari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button