Labaran siyasa

Hukumar shirya Jarabawa, WAEC ta mika wa Buhari sakamakon jarabawar sa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan dai ba neman magana ba ta yaya za a ce wai ya yi aikin soja ba tare da shaidar rubuta jarabawar WAEC ba.

Buhari ya ce sai da suka yi shekara 9 suna karatun sakandare tare da marigayi Shehu Musa ‘Yar’Adua.
” Babu yadda za ace wai har in samu damar zuwa kasashen India da Amurka karatun dabarun aikin Soji ba tare da na yi jarabawar WAEC ba.

” Sai da muka samu horo matuka a darasin Lissafi da Ilimin sanin taswirar wurare.
Duk kuma sai da aka koya mana a makaranta.

Shugaban hukumar WAEC, Iyi Uwadiae ya shaida wa shugaban kasa cewa hukumar su bata ba mutane sakamakon jarabawa sau biyu sai dai idan mutum ya rasa nasa mukan basu wani shaidar da zai nuna tabbas an yi wannan jarabawa da sakamakon da ya samu a jarabawar.

” Ina so in sanar muku cewa a bayanan mu, shugaba Buhari ya zauna jarabawar WASC a shekarar 1961 kuma yanzu haka mun zo masa da sakamakon jarabawar sa kamar yadda a ya samu a wancan lokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button