LabaraiLabaran Duniya

Hukumar NYSC ta sanar da cewa masu Bautar kasa zasu koma sansanin Horo domin kammala horinansu

Hukumar NYSC ta sanar da cewa masu Bautar kasa zasu koma sansanin Horo domin kammala horinansu.

Shugaban dake kula da yan bautar kasan, birgediya janar Shuaibu Ibrahim yace za’a bude sansanin horon a duk lokacin da gwamnatin tarayya ta bada umarni.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda ta kaima shugaban cibiyar dake kula da cututtuka a Najeriya, Dr. Chikwe Ihekweazu a ranar Talata a Abuja.
Shugaban ya kara da cewa, anrufe duk sansanin ne a lokacin da yan tsari na A suka yi sati daya da fara horo saboda karesu dake kamuwa da cutar korona.
Daga karshe yace za’a bude sansanin alokacin da cibiyar kare cuttutuka ta amince musu kuma yan tsari na A zasu koma domin ida suran kwanakin da ya rage masu a sansanin. Kuma ya roki shugaban kare cututtuka da su bada abubuwan kariya da duk sansanin yan bautan kasan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button